An Ƙara Samun Bayanai kan Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP ke Sauya Sheƙa zuwa APC
- Balarabe Akinwunmi ya bayyana cewa tsoro ne ke sanya gwamnonin PDP sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- Akinwunmi, tsohon hadimin tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen amfani da ƙarfin mulki a siyasa
- Jigon na jam'iyyar PDP ya ce Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ɗaya daga cikin waɗanda suka sha wahala a siyasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Wani jigo a PDP kuma tsohon dan takarar Ɗan Majalisar Wakilai a mazaɓar Akure ta Kudu/Akure ta Arewa, Balarabe Akinwunmi ya nuna damuwa kan sauya shekar gwamnoni.
Akinwunmi ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda wasu gwamnonin jam'iyyar PDP suka manta komai, suka zaɓi sauya sheƙa zuwa APC.

Asali: Facebook
Jigon, wanda ya kasance tsohon hadimin tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, ya ce tsoro ke sa gwamnonin PDP komawa APC, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya sa gwamnoni ke komawa APC
Ya bayyana cewa yawancin gwamnonin sun zabi sauya shaƙar ne ba don wata ƙida ba, sai dai kawai neman mafaka daga hukunci ko tona laifuffukansu na baya.
“Su gwamnonin sun fi kowa sanin abin da suke ɓoyewa amma idan ba ku manta ba, Oshiomhole ya taba cewa idan ka shiga jam’iyya mai mulki, an yafe maka zunubanka.
"Don haka su kaɗai ne suka san irin zunuban da suka aikata da suke son a rufe musu. Wata kila don haka suke komawa can.”
- Balarabe Akinwunmi.
Ya ce yawancin sauya shekar ba su da alaka da daidaito na akida ko manufa, sai dai kawai don tsira da samun kariya ta siyasa, abin da ke lalata tsarin mulki da dimokuraɗiyya.
Jigon PDP ya buƙaci a canza salon siyasa
A rahoton Guardian, jigon PDP ya ce:
“Lokaci ya yi za a kawo ƙarshen amfani da ƙarfin mulki da shugaban kasa a matsayin makamin tsoratarwa. Shugaban kasa kansa dan dimokuraɗiyya ne.

Kara karanta wannan
ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka
"Ya sha wahala a baya. An zalunce shi na tsawon shekaru. Don haka, bai kmaata a ce shugaban ko jam’iyya mai mulki su bi wannan hanyar ta azzalumai ba."
Balarabe Akinwunmi ya kuma jaddada cewa 'yancin dimokuraɗiyya da ƙarfin kaɗa kuri'a na hannun talakawa, ba a hannun masu rike da mukaman siyasa ba.

Asali: Facebook
'Ƴan Najeriya ke da karfin ɗora shugabanni'
Ya tunawa ƴan Najeriya yadda suka yi amfani da ƙarfin ƙuri'unsu wajen kifar da gwamnonin da suka nemi zama sanata duk da kuwa suna kan mulki.
“A zabukan 2023, akalla gwamnoni uku daga cikin G5 da suka tsaya takarar Sanata amma ba su samu nasara ba, sun sha kaye. Wannan zabukan sun nuna mana cewa ƙarfin zaɓe yana hannun mutane.”
Gwamnan Osun na shirin barin PDP?
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya karyata rahotannin da ke cewa yana shirin komawa jam’iyyar haɗaka watau ADC.
Gwamna Adeleke ya ce ko kaɗan bai taɓa tunanin shiga ADC ko kuma haɗa kai da wasu jiga-jigan jam'iyyar kafin zaɓen Osun na 2026 ba.
Adeleke ya bayyana irin waɗan nan jita-jita a matsayin marasa tushe, yana mai jaddada cewa yana nan daram a cikin babbar jam'iyyar adawa PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng