2027: Tinubu Ya Fara Shawo kan Arewa, An Masa Alkawarin Kuri'u a Bauchi
- Al’ummar Zaar sun bayyana farin cikinsu bisa nadin Yakubu Dogara a matsayin shugaban hukumar NCGC
- Mutanen yankin sun ce nadin Dogara ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu ke daraja yankinsu da mutanensu
- Sun sha alwashin goyon bayan Tinubu a zaben 2027 bisa la’akari da gagarumar gudummawar Dogara ga yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Al’ummar Zaar da ke jihar Bauchi sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sun fadi haka ne bisa mukamin da Tinubu ya ba tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a matsayin shugaban hukumar NCGC.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa a taron da suka gudanar a Tafawa Balewa al’ummar suka dauki matakin tare da shan alwashin sake zaben Tinubu a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar tsofaffin sojoji ta ƙaramar hukumar Tafawa Balewa, Emmanuel Peter, ne ya jagoranci taron, inda ya bayyana Dogara a matsayin gwarzon dan asalin ƙasar Zaar.
Zaar na murna da mukamin da aka ba Dogara
A cewar Emmanuel Peter, nadin Dogara ya kasance wani babban cigaba ga mutanen Zaar, domin ya nuna amincewar gwamnatin tarayya ga dan yankin.
Peter ya ce:
“Mun taru yau domin nuna farin ciki da kuma girmamawa ga ɗanmu Yakubu Dogara, wanda ya kawo wa yankinmu daukaka ta fannoni da dama.”
Ya ƙara da cewa, wannan mataki na shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa Dogara yana da ƙwarewa da amana, kuma ya yi wa mutanen Zaar aiki ba dare ba rana.
Dogara ya kawo cigaba ga yankin Zaar
Al’ummar sun jaddada cewa, tun lokacin da Dogara ya shiga siyasa, ya kasance jagora nagari wanda ya tsayu wajen ganin an samu manyan ayyuka a fannin ilimi da lafiya.
“Ya taimaka wajen samo guraben aiki na dindindin ga matasanmu a ma’aikatun gwamnatin tarayya, wanda hakan ya basu makoma mai alfanu,”
- Inji Peter.
Sun ce Dogara bai tsaya kawai da sama musu ayyuka ba, har ma ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manyan ayyuka a yankin.

Source: Facebook
Alƙawarin sake zaben Tinubu a 2027
A karshe, al’ummar Zaar sun bayyana cewa za su mayar da martani da kuri’unsu a babban zaben 2027, domin nuna godiya ga Shugaba Tinubu.
“Za mu yi amfani da zaben mai zuwa domin nuna godiya da biyayya ga gwamnatin da ke bai wa yankinmu damar taka rawa a harkokin mulki,”
- Inji Peter
Sun roki Allah ya ci gaba da kare Dogara tare da ba shi lafiya da ikon ci gaba da yi wa Najeriya hidima.
APC ta caccaki masu hadaka a ADC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da sauran masu hadaka a jam'iyyar ADC.
Kakakin APC, Felix Morka ya bayyana cewa El-Rufa'i da masu son hadaka a ADC suna cikin rudanin siyasa ne amma ba su da wata manufa.
APC ta bayyana cewa kokarin tsayar da Atiku Abubakar takara a 2027 ya saba tsarin karba karba tsakakin Kudu da Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

