'Mene aka Yi Mana?' Hadimin Ganduje Ya ce za Su Tuhumi Tinubu a Kano a 2027
- Hadimin tsohon shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya zargi Bola Tinubu da nuna wariya ga wasu yankuna, daga ciki har da Kano
- Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaza samar da ministoci masu ƙwazo kamar yadda aka gani a lokacin shugaba Buhari, kuma hakan na shafar cigaban ƙasar
- Yakasai ya ja hankalin Tinubu da ya koma irin jagorancin da ya yi fice da shi kafin zaɓe, domin ceto gwamnatinsa daga tabarbarewa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Salihu Tanko Yakasai, hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da harkokin mulki.
Tun bayan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa, Salihu Yakasai ya fara fito-na-fito da suka ga salon mulkin Tinubu, yana cewa abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata.

Source: Facebook
A wani shirin The PAP Show da aka wallafa a shafin X, Salihu ya zargi shugaban ƙasa Tinubu da sauya salon mulkinsa zuwa wanda ba ya amfani wasu yankunan ƙasar, ciki har da jihar Kano.
Dawisu: “Me Bola Tinubu ya yi wa Kano?”
Salihu ya ce irin mulkin da Tinubu ke yi yanzu yana zama barazana ga nasarar gwamnatin sa inda ya kwatanta da gwamantin Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa a zamanin shugaba Muhammadu Buhari, an samu ministoci masu ƙwazo da suka samu nasarori a aikinsu.
Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa idan Tinubu na da niyyar neman kuri’un mutanen Kano a zaɓen 2027, wajibi ne a duba irin ayyukan da ya kawo jihar.
A cewarsa:
“Idan shugaban ƙasa zai zo Kano domin neman kuri’a, waɗannan tambayoyi zan yi masa. Me ya yi wa Kano? Kuma zan kwatanta da abin da ya yi a Legas, ta fuskar ayyuka, da kuma ta fuskar nadin muƙamai.”
“Idan ka kalli tawagarsa, wa za ka ce shi ne babban minista? A lokacin Buhari, muna da wasu ministoci masu matuƙar ƙwazo.”
“Gwamnatin Tinubu tana da matsala," Salihu
Hadimin Ganduje ya cigaba da bayyana damuwa kan yadda Tinubu ya sauya daga irin jagorancin da aka san shi da shi kafin zaɓe, yana cewa hakan na shafar gwamnati yanzu.

Source: Facebook
A kalamansa:
“Ka yi ƙoƙari ka koma yadda muka sanka kafin zaɓe. Domin gaskiya, wannan shugaba da muka sani a baya, yana da damar da zai ɗaga Najeriya gaba ɗaya zuwa mataki na gaba.”
Ya bayyana cewa wannan ne hanya daya da Tinubu zai iya kankaro kansa daga hannun jama’ar Kano da sauran sassan Najeriya da aka ware.
A cewar tsohon 'dan takaran gwamnan na Kano, a yau kusan babban minista guda ake da shi daga kaf jihohin yankin Kudu maso gabashin Najeriya.
Nafisa: Pantami ya shawarci gwamntin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nemi gwamnatin tarayya ta karrama Nafisa Abdullah Aminu, daliba 'yar asalin jihar Yobe.
Nafisa ta lashe gasar TeenEagle ta duniya bayan ta doke dalibai da dama da suke amfani da harshen Turanci a matsayin yarensu a asali, sannan ta daga darajar Najeriya a gasar.
A cewar Sheikh Pantami, nasarar da Nafisa ta samu ba kawai alfahari ba ce ga jihar Yobe da Najeriya gaba ɗaya, amma shaida cewa matasan ƙasar na da hazaka matuƙa.
Asali: Legit.ng


