APC Ta Gaza Hakuri kan Atiku da El Rufa'i, Ta Fadi 'Hadarin' da za Su Kawo a 2027

APC Ta Gaza Hakuri kan Atiku da El Rufa'i, Ta Fadi 'Hadarin' da za Su Kawo a 2027

  • Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar ADC da kokarin karya tsarin mulkin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu
  • APC ta kira Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi a matsayin ‘yan siyasa marasa tsari
  • Felix Morka ya ce El-Rufai yana yunkurin haddasa rudani ne bayan rashin samun karbuwa a siyasa a yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana manyan 'yan siyasa da wadanda suka shiga jam’iyyar ADC a matsayin hadari ga zaman lafiyar Najeriya.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar APC, Felix Morka, ya fitar, jam’iyyar ta siffanta Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi a matsayin rudaddu.

APC ta zargi 'yan ADC da shirin kawo rudani
APC ta zargi 'yan ADC da shirin kawo rudani. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga|Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa APC ta ce El-Rufai yana furta kalaman da ba su dace ba ne domin ya nuna fushinsa bayan kin amince masa da mukamin minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta ce ADC hadari ce ga Najeriya

A cewar APC, jam’iyyar ADC da sababbin ‘yan siyasar da suka shiga cikinta na kokarin rusa tsarin karba-karba da ke raba mulkin shugabancin kasa tsakanin Arewa da Kudu.

Jam’iyyar ta ce hakan ne yasa ake kokarin fito da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ADC a zaben 2027, duk da cewa yanzu lokaci ne da Kudu za ta wa'adi na biyu.

APC ta kara da cewa irin wannan shiri da Atiku ya yi ne ya haddasa durkushewar jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Jam'iyyar APC ta zargi El-Rufa'i da nuna wariya

Felix Morka ya ce El-Rufai ya rasa matsayin da yake da shi a baya kuma ya zama mai tada hankali da zage-zage ba tare da mafita ba.

“Daga matsayin ministan Abuja zuwa yin zagi a kafafen sada zumunta, El-Rufai ya zama abin nazari ga masu bincike kan lalacewar siyasa,”

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, tsoho 'dan majalisar tarayya ya sauya sheka

- Inji Morka

APC ta zargi El-Rufai da nuna bambanci da kabilanci lokacin da yake Gwamna, da barin bashin Naira biliyan 284 a jihar Kaduna.

APC ta ce Atiku da Obi ba su da mafita

Jam’iyyar APC ta ce Atiku da Obi sun fadi zabe kuma ba su da wani tsari ko mafita sai zagin gwamnati.

APC ta tunatar da cewa dukkanin su sun yi alkawarin janye tallafin mai amma yanzu suna sukar gwamnatin da ke aiwatar da shi.

“Idan suna adawa da cire tallafin mai da daidaita farashin Dala, sai su fito da sababbin hanyoyin da za a maye gurbin kudin da ake kashewa,”

- Inji sanarwar.

Sanarwar ta musanta zargin El-Rufai na cewa Tinubu yana nuna kabilanci, inda ta ce shugaban kasa mutum ne da ba ya nuna wariya kuma kowa yana da wakilci a mulkinsa.

Lokacin da Peter Obi ya ziyarci Janar Babangida
Lokacin da Peter Obi ya ziyarci Janar Babangida. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Minista ya ce Tinubu ya kafu a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a 2027.

Kara karanta wannan

ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka

Keyamo ya bayyana haka ne yayin da ya ke kare wasu matakai da shugaban kasar ya dauka wajen gyara filin jirgin Legas.

Ministan ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafu a Arewa kuma yana da mutanen da za su masa aiki a yankin a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng