Wike Ya Yi Shagube ga Atiku, Ya Fallasa Dalilinsa Na Son Kafa Hadaka

Wike Ya Yi Shagube ga Atiku, Ya Fallasa Dalilinsa Na Son Kafa Hadaka

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi maganganu masu kaushi kan tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar
  • Wike ya bayyana cewa Atiku ya tattara 'yan komatsansa ne daga jam'iyyar PDP saboda ya san samun tikitin takarar shugaban kasa zai yi masa wahala
  • Hakazalika ya kuma caccaki tsohon mataimakin shugaban kasan kan yadda yake tsalle daga wannan jam'iyya zuwa wancan tun bayan fara mulkin farar hula

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kakkausar suka ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Nyesom Wike ya ce Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP ne saboda burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Wike ya soki Atiku Abubakar
Wike ya yi kalaman suka kan Atiku Abubakar Hoto: @GovWike, @atiku
Source: Facebook

Wike ya yi wannan maganar ne yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida a birnin Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

"Shawarar da zan ba Atiku da ni ɗansa ne," Ministan Tinubu ya ɗauko tarihi tun daga 1999

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya yi shagube ga Atiku

Ministan na babban birnin taraya Abuja ya yi shagube ga Atiku saboda yadda yake sauya jam’iyya tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999.

Ya bayyana cewa Atiku yana sauya sheka ne saboda burinsa kawai na darewa kan kujerar shugaban ƙasan Najeriya.

"Atiku yana cikin PDP a shekarar 1999, daga bisani ya koma jam’iyyar AC. Daga AC sai ya dawo PDP, daga baya ya tafi APC, sannan ya sake dawowa PDP, duk dai don neman takarar shugabancin ƙasa."

- Nyesom Wike

A yayin tattaunawa da manema labaran, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kuma yi watsi da hadakar jam’iyyun adawa da ake ƙoƙarin kafa wa domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC.

Wike ya fadi dalilin ficewar Atiku daga PDP

Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya fice daga PDP ne domin ya san ba zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka

"Yadda PDP take yanzu, da wuya Atiku zai samu tikitin takara, don haka ba ya jin daɗi. Daga nan sai ya fara cewa a yi hadaka domin kalubalantar Tinubu. Wannan ba daidai ba ne."
"Dalilin da ya sa yake neman hadaka shi ne saboda ya san ba zai iya samun tikitin takara a PDP ba."

- Nyesom Wike

Wike ya taso Atiku a gaba
Wike ya caccaki Atiku Abubakar Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan Wike

Wike ya roki alfarma wajen 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya mika kokon bararsa ga 'yan Najeriya.

Nyesom Wike ya bukaci 'yan Najeriya da su daure su rika sanya shi a cikin addu'a a kowace rana saboda dumbin kalubalen da yake fuskanta.

Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa yana bukatar a sanya shi cikin addu'o'in ne domin Allah ya dora shi a kan manyan mutanen da suke jin sun fi karfin doka a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng