APC Ta Yi Babban Rashi, Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka
- Shiddi Danjuma Usman ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC bayan ya shafe shekara da shekaru a cikinta
- Ya bayyana gazawar jam’iyyar wajen bin ka’idojin dimokuraɗiyya da kuma kaucewa akidun da aka kafa ta a kai
- Sai dai har yanzu bai bayyana inda zai nufa ba, amma ya ce zai ci gaba da fafutukar kawo cigaba da adalci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba – Tsohon ɗan majalisar wakilai da ya wakilci mazabar Wukari/Ibi a Jihar Taraba, Hon. Shiddi Danjuma Usman, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa Hon. Shiddi Usman ya wakilci mazabarsa a majalisar dokoki ta ƙasa a majalisun kasa na 8 da 9.

Asali: Facebook
Leadership ta wallafa cewa ya bayyana cewa ya fice ne bayan dogon tunani da ganin cewa jam’iyyar ta raba hanya da akidun da suka jawo hankalinsa a farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin fitar Hon. Usman Shiddi daga APC
A wata hira ta waya da ‘yan jarida a ranar Lahadi, Shiddi ya fadi wasu abubuwa da ya ce su ne suka janyo fitar shi a APC.
A cewar shi:
“Bayan dogon tunani da nazari mai zurfi, na yanke shawarar barin jam’iyyar APC. Tun bayan da na shiga APC a 2020, na yi wa jam’iyyar biyayya da sadaukarwa.”
Takaddama ta hana shi takarar Sanata a 2023
Shiddi ya shiga APC da nufin yin tasiri a siyasa, ya nemi kujerar Sanatan Taraba ta Kudu a zaɓen 2023.
Sai dai rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar sun jawo rikici da kara a kotu dangane da sahihancin wanda ya yi nasara a zaben fitar da gwani.
Duk da jam’iyyar ta fara amincewa da Shiddi a matsayin ɗan takararta, wani dan takara, Sanata David Jimkuta, ya kai kara kotu yana kalubalantar sakamakon zaben.

Asali: Twitter
An fara shari'a tun daga matakin kasa har zuwa Kotun Ƙoli, kuma daga karshe Kotun ta amince da Jimkuta a matsayin ɗan takara na gaskiya na jam’iyyar.
Tribune ta wallafa cewa yayin jawabin sauya sheka, ya ce:
“Na bar jam’iyyar ba tare da ina kiyayya da ita ba, sai dai ina fatan cewa sabon babin da zan fara zai kasance daidai da burin jama’ar da nake wakilta.
"Fafutukar neman adalci, gaskiya da ci gaba ba ta tsaya a nan ba,”
Hon. Usman Shiddi ya koma ADC ne?
Duk da ficewarsa daga jam’iyyar APC, Shiddi bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba ko makomar siyasarsa gaba ɗaya.
Sai dai a halin yanzu, 'yan adawa na cigaba da ƙarfafa gwiwar juna yayin da zaben 2027 ke kara ƙaratowa, inda suke hasashen sauyin mulki daga jam’iyyar APC.
Sanata Yar'adua ya fita daga APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Abubakar Sadiq Yar'adua ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Abubakar Sadiq Yar'adua ya sauya sheka ne bayan shafe shekaru a APC.
Legit Hausa ta rahoto cewa Sanatan ya koma jam'iyyar ADC domin hada kai da su Atiku Abubakar da sauran manyan 'yan adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng