2027: Bayan Hukuncin SDP, Jam'iyyar ADC Ta Mika Bukata ga El Rufa'i

2027: Bayan Hukuncin SDP, Jam'iyyar ADC Ta Mika Bukata ga El Rufa'i

  • Jam’iyyar ADC a Kaduna ta bukaci jigo a SDP, Nasir El-Rufai da ya sauya sheka zuwa sabuwar haɗakar siyasa
  • Ƙusa a jam'iyyar ADC, Salihu Mohammed Lukman ya ce yanzu lokaci ne na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceto Najeriya
  • Ya ce dole ne ƴan adawa su ajiye bambance-bambancensu matukar ana son a kai jam'iyyar APC kasa a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Jam’iyyar ADC reshen jihar Kaduna ta bukaci tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, da ya fice daga jam’iyyar SDP tare da magoya bayansa.

Ta bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata tsohon gwamnan ya shigo ADC a hukumance domin karfafa haɗakar adawa a jihar da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
ADC ta nemi El-Rufa'i ya dawo cikinta Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

The Nation ta walllafa cewa wani jigo a jam’iyyar ADC kuma tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ne ya bayyana hakan..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kiran ne yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Lahadi, 4 ga Agusta, 2025 inda ya ke ganin akwai bukatar a hade.

ADC na gayyatar El-Rufai da magoya bayansa

Rahoton ya ci gaba da cewa Lukman ya ce jam’iyyar ta ADC ta buɗe kofarta ga kowa domin haɗa ƙarfi da ƙarfafa jam’iyyar adawa, musamman a jihohi kamar Kaduna.

Ya bayyana cewa El-Rufai na daya daga cikin jiga-jigai a tafiyar haɗakar siyasar kasa saboda haka dawowarsa ADC za ta taimaka sosai.

Jiga-jigan haɗakar adawa
ADC ta ce yanzu lokaci ne ya haɗa kai Hoton: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

“'Kofar ADC a bude ta ke ga kowa. Kusan watanni uku da suka gabata, 'yan siyasa akalla 10,000 sun shiga jam’iyyar, sannan wata guda da ya gabata, 'yan NNPP da PDP fiye da 5,000 sun shigo cikimu."

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, tsoho 'dan majalisar tarayya ya sauya sheka

Ya bayyana cewa har yanzu El-Rufai ba 'dan ADC ba ne, amma yana daga cikin shugabannin haɗakar kuma mutum ne mai matukar muhimmanci a tafiyar.

ADC na shirin kara karfi kafin 2027

Lukman ya ce a halin yanzu ana ci gaba da yin rijista ga sababbin 'yan jam’iyyar ADC ta hanyar intanet a matakin kasa, kuma yana kira ga ‘yan Najeriya su shiga domin a tsira tare a 2027.

Ya ƙara da cewa barazana ce babba idan aka bar APC kadai ta ci gaba da mulki ba tare da ƙalubale daga wata jam’iyyar adawa ba.

Ya ce:

“Mun fahimci cewa babu wata jam’iyya da za ta iya kayar da APC a matakin tarayya ko jihohi idan ba tare da haɗin kai ba. Saboda haka mun yanke shawarar cewa dole ne a fara da haɗa kai, ba tare da batun burin mutum ba.”

Jam'iyyar SDP ta kori Nasir El-Rufa'i

Kara karanta wannan

El Rufai ya hango babbar matsalar da za ta auku idan APC ta ci gaba da mulkin Najeriya

A baya, kun ji cewa jam’iyyar SDP ta sanar da dakatar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga mu’amala da jam’iyyar na tsawon shekara 30.

Wannan hukunci ya fito ne daga Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar bayan kammala bincike kan zarge-zargen da ake yi masa. Daga cikin abubuwan da ake zarginsa da yi har da alakar siyasa da sabuwar jam’iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC mai fafutukar ƙwace mulki a zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.