2027: An Yi wa 'Yan Arewa Gargadi da Rabuwar Najeriya kan Tazarcen Tinubu
- Reno Omokri ya bukaci shugabannin Arewa su ba Bola Tinubu damar kammala mulkinsa domin zaman lafiyar kasa
- Ya ce a baya an hana shugaba Goodluck Jonathan damar wa'adi na biyu, lamarin da ya haifar da tarzoma a yankin Niger Delta
- Omokri ya ce Arewa na amfana da ayyuka da shirye-shiryen Tinubu, ciki har da manyan tituna da tallafin karatu ga dalibai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Najeriya - Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya roki 'yan yankin Arewa da su ba shugaban kasa Bola Tinubu damar yin wa'adin na biyu.
Omokri ya ce Najeriya kasa ce mai rauni, saboda haka kada a bar muradin wasu 'yan siyasa ya hana zaman lafiyar kasar.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a X, ya ce hana Goodluck Jonathan samun wa'adi na biyu a 2015 ya jefa kasar cikin rikici da koma bayan tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kafa dalili da cewa Arewa na cin moriyar gwamnatin Tinubu kuma bai kamata su dakile burin shugaban kasar na samun wa'adi na biyu ba.
Doke Goodluck Jonathan da tattalin Najeriya
Reno Omokri ya bayyana cewa hana Goodluck Jonathan wa'adi na biyu a 2015 ya haddasa tabarbarewar tsaro da koma bayan tattalin arziki a Najeriya.
Ya ce hakan ya haifar da farfadowar tarzoma da satar danyen mai a yankin Niger Delta, wanda ya rage yawan mai da Najeriya ke fitarwa da kashi 50 cikin 100.
Ya kara da cewa hakan ne ya jefa kasar cikin koma baya sau biyu a lokacin mulkin Buhari, inda ta zamo cibiyar talauci ta duniya da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Omokri ya ce Tinubu ya yi ayyuka a Arewa
A cewarsa, a yanzu Najeriya na farfadowa karkashin Bola Tinubu, inda ya ce bashin kasar ya ragu daga dala biliyan 113.7 zuwa 97.
Ya ce kudin da ake rabawa jihohi sun ninka na lokacin Buhari, sannan kuma shirin lamunin dalibai ya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa.
Ya ce ana gina manyan tituna kamar Sokoto-Illela-Badagry da sauransu, da kuma karin wasu muhimman ayyuka a yankin.

Source: Facebook
Barazanar ballewa daga Najeriya
Omokri ya ce tun bayan samun 'yancin kai, yankin Kudu bai taba hana shugaba daga Arewa ya kammala wa'adinsa ba, don haka bai kamata a sake maimaita abin da aka yi wa Jonathan ba.
Ya gargadi shugabannin Arewa da kada su haifar da wani sabon yunkurin ballewa daga Kudu kamar yadda ake fama da shi a Kudu maso Gabas.
Ya kuma bayyana cewa ya kamata shugabannin Arewa su dauki darasi kan abin da ya faru a Rasha, Yugoslavia da Sudan inda wasu suka balle daga kasashen.
Ya ce Tinubu ya nuna biyayya da goyon baya ga Buhari, don haka ya cancanci samun irin wannan goyon bayan daga Arewa.
An zargi Obi da shirin kifar da gwamnatin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa hadimin Peter Obi ya karyata cewa suna shirin yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Hadimin na Obi ya ce ya kamata hukumar DSS ta cafke wanda ya yi zargin domin ya amsa tambayoyi.
Rahotanni sun nuna cewa wani dan tsagin jam'iyyar LP ne ya ce Obi da shugaban kwadago suna son kifar da gwamnatin Tinubu da karfi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

