Bayan Ya Baro PDP, Sanata Melaye Ya Kawo Hanyar da ADC Za Ta Buga Tinubu da Ƙasa a 2027

Bayan Ya Baro PDP, Sanata Melaye Ya Kawo Hanyar da ADC Za Ta Buga Tinubu da Ƙasa a 2027

  • Sanata Dino Melaye ya bayyana burinsa game da ɗan takarar da ADC za ta ba tikitin shugaban ƙasa a zaɓen 2027
  • Tsohon sanatan Kogi ta Yamma ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen lalubo wanda zai iya buga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ƙasa a zaɓe
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa ADC baya domin ita ce jam'iyyar da ta zo domin tsamo su daga duhu zuwa haske

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana cewa jam'iyyar haɗaka za ta zaƙulo ɗan takarar da zai iya tumurmusa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Sanata Melaye ya ce duk da haɗakar ADC ta tara manya-manyan jiga-jigan adawa, jam'iyyar ta shirya tsayar da wanda zai ba mara ɗa kunya a zaɓen da ke tafe.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Sanata Dino Melaye.
Dino Melaye ya bayyana ɗan takarar yake fatan ADC ta tsayar takarar shugaban ƙasa Hoto: @DinoMelaye
Source: Twitter

Dino Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane ɗan takara ya kamata ADC ta tsayar?

“Mu da muke cikin ADC muna bukatar mu samar da dandalin siyasa mai daɗi da kuma kwanciyar hankali. Ina da tabbaci cewa wannan dandali zai samar da dan takarar shugaban kasa da zai buga Shugaba Tinubu da ƙasa a 2027.”
“Amma na ɗauki alƙawari cewa ba zan fara magana kan wani ɗan takara ko masu sha’awar tsayawa takara ba, har sai mun tabbatar da cewa jam’iyyar ta daidaita sosai.
"Sannan muna sa ran jam'iyyar haɗaƙa za ta shirya zaɓen fidda gwani na gaskiya wanda zai fito da dan takarar shugaban ƙasar da muke fatan da ikon Allah, shi zai zama sanadin kawo sauyi.

- Sanata Dino.Melaye.

A ranar 2 ga Yuli, haɗakar ‘yan adawa da ta ƙunshi manyan jiga-jigan siyasa ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin za su yi amfani da shi wajen kalubalantar APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta yi bayani kan rashin sauya sheƙar El Rufa'i da Obi har yanzu

Taron kaddamar da hadaka a Abuja.
Dino Melaye ya roƙi duk ɗan Najeriya mai kishin ƙasa ya shiga ADC Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Dino Melaye ya haska wa ƴan Najeriya ADC

Manyan ƴan siyasar da ke cikin haɗakar sun kunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, da sauransu.

Vanguard ta rahoto cewa yayin da yake tsokaci kan ƙarfin haɗaka, Dino Melaye ya ce ADC jam'iyya ce ta ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da burin kawo sauyi.

“Ina so ‘yan Najeriya su fahimci cewa ADC wani mimbari ne na ƙasa. Kamar yadda ake wa'azi a coci mutanen da ke son barin duhu su koma haske ke amsawa to haka ADC take," inji shi.

Atiku ya samu goyon baya kafin 2027

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ECK Foundation, Dr. Emeka Kalu, ya tsoma baku kan batun tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kalu ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ne kaɗai wanda zai iya ceto Najeriya daga ƙangin tattalin arziki da matsalar tsaro.

A cewarsa, gogewa da jajircewar Atiku ne suka sanya shi ya zama fitaccen dan takara da zai iya doke Shugaba Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262