Matasan Arewa Sun Fara Kawo Wa Shugaba Tinubu Tangarɗa kan Shirin Canza Shettima a 2027

Matasan Arewa Sun Fara Kawo Wa Shugaba Tinubu Tangarɗa kan Shirin Canza Shettima a 2027

  • Matasan Arewa maso Gabas sun nuna damuwa kan yadda jita-jita ke yawo cewa Bola Tinubu na iya canza abokin takara a 2027
  • Ƙungiyar matasan ta ce sauya Shettima na iya kawo hargitsi a jam'iyyar APC tare da barazana ga tazarcen shugaban ƙasar a 2027
  • Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya tabbatar da lamarin ga wakilin Legit Hausa, inda ya ce babu dalilin canza Shettima

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Ƙungiyar Matasan APC na Yankin Arewa maso Gabas ta yi gargaɗi kan jita-jitar sauya mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a zaɓen 2027.

Matasan sun gargaɗi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya guji sauya Shettima, domin hakan na iya jefa tazarcen da zai nema a gagarumar matsala.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Matasan Arewa maso Gabas sun harzuka da yunƙurin canza Shettima a 2027 Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Shugaban ƙungiyar matasan APC na Arewa maso Gabas, Kabiru Garba Kobi ne ya bayyana hakan ga wakilin Legit Hausa a Bauchi yau Juma'a.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin canza Shettima ya fusata matasan APC

Kabiru Kobi ya ce suna Allah wadai da labarin da ake yaɗawa na canza Shettima, wanda a cewarsa zai iya tayar da hargitsi a APC tun kafin zaɓen 2027.

Ya ce wannan yunkuri zai iya lalata haɗin kan jam’iyyar APC kuma zai iya zama barazana ga nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar su koyi darasi daga kura-kuran baya, su guji rikice-rikicen cikin gida kamar yadda ya faru da PDP a 2015.

APC na iya shiga rikici saboda canza Shettima

A cewarsa, tawagar matasan APC tana goyon bayan maimaita tikitin Tinubu-Shettima a 2027, inda ya bayyana su da cewa "an gwada su kuma jama'a sun aminta da su."

“Duk wani yunkuri na sauya tikitin Tinubu-Shettima a 2027 zai haifar da ƙiyayya da za ta iya wuce lokacin zaɓe, yana kuma da haɗarin da zai iya hana jam’iyya nasara.”

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

“Kowa ya san abin da ya faru da PDP a baya shi ne har yanzu yake binta, duk wanda bai ji bari ba, ba zai ƙi gani ba.

- Kabiru Garba Kobi.

Matasan Arewa maso Gabas sun faɗi matsayarsu

Kungiyar ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da tallata tikitin Tinubu-Shettima, tare da kira ga 'ya’yan jam’iyyar APC su haɗa kai da su don cimma nasara.

Kabiru ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman yadda ya nuna jarumtaka wajen yanke ɗaukar matakan farfaɗo da tattalin arziki.

Matasa sun yi fatali da masu so a canza Shettima.
Matasa sun bukaci Tinubu ya yi watsi da masu kiran ya canza Kashim Shettima Hoto: Abdullahi Abubakar
Source: Facebook

Shugaban matasan ya tabbatar da koke na su ga wakilin Legit Hausa, yana mai cewa mutanen Arewa maso Gabas sun gamsu kuma suna tare da Shettima 100%.

Ya ce a tarihin dimukraɗiyya, ba su taɓa jin inda aka canza mataimakin shugaban ƙasa haka kurum ba tare da ya ci amanar ƙasa, ya ci amanar uban gidansa ba.

Kabiru Garba ya shaida mana cewa:

"Mu mutanen Arewa maso Gabas muna tare da Shettima, ba irin wakilcin da zai mana wanda bai mana ba, shiyasa muna Allah wadai da masu kiran da canza shi."

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar ATT ta samo mafita ga Arewa kan tazarcen Shugaba Tinubu

"Muna Allah wadai da masu yaɗa labarin da kiran a canza Shettima, mu a Arewa maso Gabas ba mu da gwani da zaiɓiya wakiltar jama'a kamar Shettima.

Matasan APC za su tarawa Tinubu ƙuri'u

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya ce sun bullo da hanyar kara sama wa shugaban kasa, Bola Tinubu kuri'a a 2027.

Dayo Israel ya kuduri aniyar jawo hankalin karin matasa su shiga jam’iyyar APC, tare da kokarin samar dankuri’u miliyan 10 ga Shugaba Tinubu.

Ya ce nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Tinubu ke samu a tsakanin matasa ne suka ba shi kwarin guiwa da sha’awar wannan aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262