An Zo Gaɓar Ƙarshe kan Batun Sauya Sheƙar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC

An Zo Gaɓar Ƙarshe kan Batun Sauya Sheƙar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC

  • Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Bebeji da Ƙiru ya kawo karshen raɗe-raɗin Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC mai mulki
  • Hon. Abdulmumini Kofa ya ce jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ne kaɗai zai yanke hukuncin karshe kan shiga APC ko akasin haka
  • Jagoran na NNPP a Kano ya bayyana cewa kowa ya san shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Kwankwaso abokanan juna ne tun da daɗewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji ta Jihar Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa, ya yi bayani kan batun sauya sheƙar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Abdulmumini Kofa ya ce Kwankwaso kaɗai ke da ikon yanke shawarar ko zai sauya sheka zuwa APC ko zai ci gaba da zama a NNPP.

Abdumumini Jibrin Ƙofa tare da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso.
Dan Majalisar Tarayya daga Kano ya ce Kwankwaso ne ke da ikon yanke hukuncin karshe kan sauya sheƙarsa zuwa APC Hoto: @AbdulAbmj
Source: Twitter

Ɗan Majalisar ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon DW bayan ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jitar Kwankwaso zai shiga APC ta yi karfi

Hon. Abdulmumini ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba da ta gabata, kuma sun tattauna kan ɓatutuwa da dama.

Sai dai wannan ganawa ta sake tayar da jita-jitar sauya sheƙar Kwankwaso duba da alaƙar da ke tsakanin Abdulmumimi Kofa da jagoran NNPP.

Wasu na ganin wannan ziyara da ɗan Majalisar ya kai na da alaƙa da tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangaororin biyu domin shawo kan Kwankwaso ya koma APC.

Alaƙar Kwankwaso da Shugaba Tinubu

Amma da yake martani a hirar da Daily Trust ta tattaro, Hon. Abdulmumini Jibrin ya ce:

“Wannan zuwan da na yi wurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba abin mamaki ba ne. Kowa ya san dangantakarmu da shugaban ƙasa.
"Haka kuma, kowa ya san dangantakar da ke tsakanin Bola Ahmed Tinubu da jagoranmu, Rabiu Musa Kwankwaso, kowa ya san abokanan juna ne.

Kara karanta wannan

Jibrin Kofa: NNPP ta yi magana bayan dan Kwankwasiyya ya gana da Tinubu

Kwankwaso kaɗai zai iya yanke hukunci

Dangane da jita-jitar da ake yaɗawa kan sauya shekar Kwankwaso, Kofa ya ƙara da cewa:

“Wannan batu ya fi ƙarfi na, ba zan iya magana kan cewa Kwankwaso zai koma APC ba, wannan magana ce ta Kwankwaso, shi ne zai iya yanke wannan hukuncin.
"Haka nan magana ce da ta shafi shugaban ƙasa, ni karamin yaro ne, ba zan sa baki kan abin da ya shafi waɗannan manya manyan mutane ba amma idan aka zo gaɓar sulhu, shi sulhu alheri ne.
"Kowa ya san ni ba munafiki ba ne, idan akwai wata magana da na tattauna da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya kamata na gayawa jagoranmu Kwankwaso, zan gaya masa.
"Shi ma idan ya bani saƙo na gaya wa shugaban ƙasa, zan faɗa masa, wannan ba matsala ba ne a wuri na."

- In ji Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa.

Abdulmumini Jibrin Kofa ya haɗu da Shugaba Tinubu.
Kofa ya ce ba zai iya yanke hukunci kan yiwuwar Kwankwaso ya koma APC ba Hoto: @AbdulAmj
Source: Twitter

NNPP za ta hukunta Abdulmumini Kofa?

A wani labarin, kun ji cewa NNPP ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na hukunta Abdulmumini Jibrin Kofa saboda ya gana da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya ce abin da ɗan Majalisar Kiru da Bebeji ya yi bai saɓawa dokokin jam'iyya ba.

Johnson ya bayyana cewa babu wani abu da Jibrin ya aikata da za a iya cewa ya sabawa jam’iyyar, domin an san da ganawar tun kafin ta faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262