Bayan Zargin Shirya Yi wa Tinubu Juyin Mulki, Ana so Hukuma Ta Dauki Mataki
- Hadimin Peter Obi ya karyata zargin cewa maigidansa na shirin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu
- Valentine Obienyem ya bayyana zargin a matsayin abin dariya, hatsari da kuma rashin sanin ya kamata kwata kwata
- Lura da irin girman zargin, hadimin ya ce bai kamata a bar wanda ya yi shi ba tare da hukuma ta kama shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abua – Hadimin tsohon ɗan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi, ya maida martani kan zargin cewa maigidansa yana kitsa kifar da gwamnatin Bola Tinubu,
Hadimin Peter Obi ya yi magana yana mai cewa wannan zargi rashin hankali ne aka yi shi da sunan siyasa.

Asali: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Valentine Obienyem ya bayyana cewa zargin juyin mulki da wani mai suna Abayomi Arabambi ke yadawa, barazana ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi zai yi wa Tinubu juyin mulki?
A wata sanarwa da ya fitar, Obienyem ya ce Abayomi Arabambi ya shigar da ƙorafi ga hukumomin tsaro kan zargin kifar da gwamnati.
Obienyem ya ce ana zargin Peter Obi, shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero, Sanata Victor Umeh, da wasu daga ɓangaren Nenadi Usman, da shirin kifar da gwamnatin Tinubu.
Ya ce:
“Wannan zargi ba wai abin dariya ba ne kawai, illa ce ga zaman lafiyar ƙasa. Meyasa har yanzu ba a kama wanda ya kawo wannan ƙorafi ba?
“Shirin juyin mulki babban laifi ne na tsaron ƙasa. Zargin mutum da haka ba tare da shaidar kwarai ba, musamman mashahuran mutane, cin fuska ne da tayar da zaune tsaye.
“Idan muna a ƙasar da akwai tsari, to dole a kama wanda ya kawo wannan ƙorafi domin a tabbatar da inda ya samo wannan zargi kuma ya bayyana shaidunsa.”
An nemi binciken wanda ya yi zargin
Obienyem ya yi mamaki kan yadda aka yi watsi da batun, inda ya nemi a binciki Arabambi sosai ko dai a tabbatar da zargin ko kuma a hukunta shi bisa yaɗa ƙarya mai hatsari.
“Idan kuwa, kamar yadda muke gani, wannan wata makarkashiyar siyasa ce kawai, to dole ne a hukunta wanda ya yi ƙaryar nan domin hana irin hakan gaba.”
Legit ta rahoto ya ƙara da cewa:
“Ba a amfani da kalmar juyin mulki a matsayin habaici ko tsokana a siyasa. Wannan kalma tana nuni da cin amanar ƙasa.
"Rashin da’a wajen amfani da ita na iya haddasa rikici, rasa rayuka da kuma rushe tsarin gwamnati.”

Asali: Twitter
Tun a karon farko Punch ta rahoto cewa daya daga cikin jagororin tsagin Abayomi Arabambi ne ya zargi Obi da kitsa juyin mulki.
El-Rufa'i ya yi magana kan takarar Obi
A wani rahoton, kun ji cewa dan tsohon gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufa'i ya yi magana kan takarar Peter Obi.

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
Bashir El-Rufa'i ya bayyana cewa Peter Obi zai fi Atiku Abubakar samun damar kifar da Bola Tinubu idan suka gwabza a 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shiga hadaka karkashin jam'iyyar ADC domin tunkarar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng