2027: Dino Melaye da Wasu Na Hannun Daman Atiku 2 da Suka Fice daga PDP zuwa ADC
- Kawancen 'yan adawa na kara karfi a Najeriya karkashin jagorancin, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi
- A ranar 16 ga Yulin 2025, Atiku ya fice daga PDP, inda ya ce akwai sabani da ba za a iya shawo kansu ba tsakaninsa da jam’iyyar
- A rahoton nan, Legit Hausa ta jero jiga-jigan na hannun damar Wazirin Adamawa da suka bar PDP zuwa ADC, ciki har da Dino Melaye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – A kwanan baya ne jagoran adawa a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance.
Atiku na hada kai da wasu jiga-jigan ’yan adawa domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyarsa mai mulki ta APC a zaben 2027.

Source: Twitter
Shirin Atiku na tunkarar zaben 2027
Kodayake Atiku na cikin hadakar da ta kaddamar da ADC, amma Legit Hausa ta rahoto cewa bai sauya sheka zuwa jam’iyyar ba a hukumance.

Kara karanta wannan
Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun kafin ya juya wa PDP baya, jam’iyyar da ya tsaya mata takarar shugaban kasa a zabukan 2019 da 2023, Atiku tare da 'yan adawa suka ayyana ADC matsayin jam'iyyar hadakarsu.
Wasu daga cikin abokan siyasar Atiku sun mara masa baya na shiga hadakar, kuma sun yi koyi da shi wajen ficewa daga jam'iyyar PDP.
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta duba jerin wasu mutane uku daga cikin manyan na hannun daman Atiku da suka sauya sheka daga PDP zuwa ADC.
Na hannun daman Atiku da suka koma ADC
1. Sanata Dino Melaye
Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ajiye katin shaidarsa ta zama dan PDP, inda ya zargi jam’iyyar da gazawa wajen zama babbar jam'iyar adawa a Najeriya.
A wata wasikar murabus da ya aika wa shugabancin PDP, wacce aka gani a ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2025 Dino Melaye ya ce ba zai iya ci gaba da shiga ayyukan jam'iyyar ba.
A cikin wasikar, Legit Hausa ta ruwaito Dino Melaye ya bayyana cewa:
“Na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP daga yau. Wannan mataki ya zama dole saboda jam’iyyar ta rasa karfi da damar ceto ‘yan Najeriya daga halin da ake ciki.”
Bayan haka, Melaye ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X (Twitter), inda ya rubuta: “SDM Fully ADC,” wanda ke nuna ya shiga sabuwar jam’iyyar hadaka.
2. Aliyu Bello
Aliyu Bello, sakataren kudi na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ya ajiye mukaminsa sannan kuma ya fice daga jam’iyyar.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Alhaji Aliyu Bello ya koma ADC domin shirye-shiryen zaben 2027.
Alhaji Aliyu, wanda ya shafe dogon lokaci a PDP kuma amini ne ga Atiku, ya aika da wasikun murabus guda biyu a ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025 – daya zuwa shugaban PDP na jihar Kaduna, daya kuma zuwa shugaban PDP na mazabarsa ta Tudun Nupawa.
A cikin daya daga cikin wasikun, ya rubuta cewa:
“Na rubuto wannan wasika ne domin sanar da murabus dina daga matsayin sakataren kudi na PDP a jihar Kaduna, wanda zai fara aiki daga ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025.”

Source: Twitter
3. Hon. Musa Elayo Abdullahi
A kwanan nan, muka ruwaito cewa tsohon karamin ministan shari’a kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben Atiku na 2023, Musa Elayo, ya fice daga PDP bayan shekara 26 da kasancewa a jam’iyyar.
Ya aike da wasikar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 10 ga Yuli, 2025 zuwa ga shugaban PDP da sakataren mazabarsa ta Iwagu da ke karamar hukumar Keana a jihar Nasarawa.
A wasikar, Elayo ya bayyana cewa:
“Na yanke wannan shawarar ne bayan zurfin tunani da nazari dangane da akidun siyasa da manufofi na.”
Bayan ficewarsa daga jam'iyyar APC, tsohon ministan ya kuma sanar da komawarsa jam'iyyar hadaka ta ADC.
A ranar Laraba, 30 ga Yuli, rahotanni suka bayyana cewa Elayo ya zama sabon mataimakin shugaban ADC na kasa mai kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje. Sai dai Legit.ng ba ta iya tabbatar da hakan ba zuwa yanzu.
'Yan takarar gwamna sun bar PDP zuwa ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsofaffin 'yan takarar gwamna a Ondo, Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi, sun fice daga jam'iyyar PDP a hukumance.
Eyitayo Jegede da Cif Agboola Ajayi yanzu sun shiga haɗakarsu Atiku Abubakar da ke neman kalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Sauran manyan jiga-jigan da suka sauya sheƙa zuwa ADC sun haɗa da tsohon sanatan Ondo ta Kudu, Nicholas Tofowomo, kamar yadda suka bayyana a wani taro a Ondo.
Asali: Legit.ng


