Shirin Kayar da Tinubu Ya Kankama, An Bayyana Wanda Zai Iya Gyara Najeriya a 2027

Shirin Kayar da Tinubu Ya Kankama, An Bayyana Wanda Zai Iya Gyara Najeriya a 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar na kara samun goyon bayan manyan mutane kafin zaɓen 2027
  • Shugaban gidauniyar ECK Foundation, Dr. Emeka Kalu ya ce Atiku ne kaɗai wanda zai iya ceto Najeriya daga ƙangin tattalin arziki
  • Ya kuma buƙaci al'ummar Kudu maso Gabas su marawa Wazirin Adamawa baya domin hakan zai buɗewa ɗansu Peter Obi damar mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban ECK Foundation, wata kungiya mai zaman kanta, Dr. Emeka Kalu, ya bayyana ra'ayinsa kan wanda ya dace ya karɓi mulkin Najeriya a zaɓen 2027.

Kalu ya ce tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na da kwarewar da ake bukata domin ceto Najeriya daga halin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da take ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaban matasa ya fito da ƙarfi, zai nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Emeka Kalu ya bayyana Atiku a matsayin wanda zai iya ceto Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kalu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a birnin Abuja.

Atiku Abubakar ya samu ƙarin goyon baya

Kalu ya ce gogewa da jajircewar Atiku ne suka sanya shi ya zama fitaccen dan takara da zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Ya kuma nemi yankin Kudu maso Gabas su goyi bayan Atiku, yana mai cewa hakan zai bude hanya ga Mr. Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023.

A cewarsa, idan Atiku ya samu nasara to ba shakka Peter Obi zai cika burinsa na zama shugaban kasa nan gaba, wanda hakan zai bai wa al’ummar Ibo dama a tsarin mulkin Najeriya.

Wace irin gogewa Atiku yake da ita?

Kalu ya dage cewa lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban kasa, ya nuna bajinta a fannin bunkasa tattalin arziki, jawo masu zuba jari daga waje da kuma samar da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027

Ya kara da cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na da hazaka ta siyasa da zai iya hada kan yankuna daban-daban a Najeriya, wanda hakan ya dace da bukatar kasar nan ta samun shugaba ɗaya da zai daidaita al’umma.

An hango ci gaban Najeriya a mulkin Atiku

A rahoton The Sun, shugaban na ECK Foundation, Dr. Emeka Kalu ya ce:

“Shugabancin Atiku zai kawo gagarumin ci gaba a fannin zuba jari, gine-gine, tsaro, kuma zai dawo da karfin tattalin arzikin Najeriya da ke tabarbarewa.
"Haka kuma, Atiku mutum ne da ba ya son kabilanci, wanda zai iya hada al’umma wuri guda. Abin takaici, rikice-rikicen kabilanci sun daɗe suna addabar siyasar Najeriya.”
Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.
An ba ƴan Najeriya shawarar su zaɓi Atiku a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 Hoto: @Atiku, @OfficialABAT
Source: Facebook

A karshe, Kalu ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin jam’iyyun adawa, yana gargadi cewa kowace haɗaka aka yi ba tare da manufa guda ba, to ba za a kai ga nasara ba.

Atiku na da yakinin nasarar ADC a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana yaƙininsa cewa jam’iyyar ADC za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ADC na da ingantaccen tsari da akida don ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arzikin da tsinci kanta a ciki.

Atiku ya ƙara da cewa a halin yanzu siyasar Najeriya ta canza, kuma yanzu akwai jam’iyyu da dama da ba su da akida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262