Sabuwar Rigima Ta Ɓarke a Haɗakar Su Atiku, Jigon ADC Ya Naɗa Kansa Shugabanci

Sabuwar Rigima Ta Ɓarke a Haɗakar Su Atiku, Jigon ADC Ya Naɗa Kansa Shugabanci

  • Jam'iyyar haɗaka watau ADC na ci gaba da fuskantar ƙalubale tun bayan haɗewa da tawagar jagororin adawa karƙashin Atiku Abubakar
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe a inuwar jam'iyyar ADC, Nafi'u Bala ya ce abin da haɗakar ƴan adawa ta yi tamkar fashin jam'iyya ne
  • Ya ce shi da sauran mambobin ADC masu kishin jam'iyyar za su ƙalubalanci jagorancin David Mark a gaban kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Sabon rikici ya ɓarke a jam'iyyar ADC, wacce ƴan adawa suka zaɓa a matsayin dandalin da za su kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓen 2027.

Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar ADC a jihar Gombe, Nafi'u Bala ya ayyana kansa a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe, Nafi'u Bala.
Jigon ADC daga jihar Gombe ya lashi takobin ƙwato jam'iyyarsu daga hannun ƴan haɗaka Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

Jigon ADC ya sanar da wannan mataki da ya ɗauka ne a taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba, a Abuja, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Babu mai dakatar da mu," An shirya kawo wa Tinubu, APC miliyoyin ƙuri'u a Kano a 2027

ADC ta dare gida biyu kafin zaɓen 2027

Nafi'u Bala, tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa, ya zargi tsagin da David Mark ke jagoranta da ƙwace jam'iyyar ba bisa ka’ida ba wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

A watan da ya gabata, wasu ’yan adawa da shugabannin ADC sun amince da amfani da jam’iyyar a matsayin dandalin haɗakar jam’iyyu don tunkarar zaɓen 2027.

Wasu daga cikin waɗanda ke cikin wannan haɗaka sun haɗa da, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan ƙusoshi na cikin tawagar haɗakar ƴan adawa.

A ranar 2 ga Yuli, Ralph Nwosu, wanda ya kafa jam’iyyar kuma tsohon shugaban ADC na ƙasa, ya sanar da murabus ɗin kwamitin gudanarwa (NWC) tare da goyon bayan kwamitin riƙo da David Mark ke jagoranta.a

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

Jigon ADC ya yi barazanar kai ƙara kotu

Nafi'u Bala ya bayyana cewa masu kishin ADC za su ƙalubalanci wannan ƙarfa-ƙarfa na ƙwace jam'iyyarsu da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a gaban kotu, in ji Punch.

"Muna jan hankalin ƴaƴan jam'iƴyarmu da ƴan Najeriya gaɓa ɗaya kan wannan ƙarfa-ƙarfa da aka mata ido na ganin iso, an karɓe mana shugabanci jam'iyya da rana tsaka.
"Muna kallon wannan abin kunya da wasu shugabanni suka yi, ba tare da tunanin komai ba suka jefa jam'iyyarmu cikin rigimar shugabanci.
"Mun yi Allah wadai da wannan abin kunya na sayar da makomar jam’iyyarmu ga wasu ’yan waje da ba su da alaƙa ko ta nesa da ADC.
"A tarihin dimokuraɗiyya a duniya, ba taɓa ganin shugabannin jam'iyya sun miƙa ragamar jagoranci wasu da ba ƴan wannan jam'iyya ba, ba taɓa irin haka a duniya ba.

- In ji tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe, Nafi'u Bala.

Hadakar yan adawa ta fara rabuwa kashi-kashi.
Jam'iyyar haɗaka. ADC da dare gida biyu, an samu sabon shugaban jam'iyya na ƙasa Hoto: Atiku Abubakar, Nafi'u Bala
Source: Facebook

A ƙarshe, Nafi'u ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta amince wa da shi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa.

Kara karanta wannan

ADC: Wata sabuwa ta taso a haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai tun kafin zaben 2027

2027: ADC ta musanta goyon bayan Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa Jam’iyyar ADC ta fito ta ƙaryata batun cewa an kafa hadaka ne domin cika burin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Sakataren Yaɗa Labarai na ADC ta kasa, Bolaji Abdullahi ya ce maganar cewa ADC wata kafa ce da aka gina domin cika burin Atiku, ƙage ne mara tushe.

Ya kuma tabbatarwa ƴan Najeriya a halin yanzu, babu wani ɗan takara da ADC ke goyon baya, yana mai cewa babu wanda za a ba fifiko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262