'Kafin 12:00 na Rana': Hon. Gudaji Kazaure Ya Faɗi Abin Zai Faru da Tinubu a Zaɓen 2027
- Tsohon ɗan majalisa Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu, yana zargin ta lalata Najeriya gaba ɗaya a cikin ɗan lokaci
- A cewar 'dan siyasar na Jigawa, idan Allah ya kai mu zaben 2027, kafin ƙarfe 12:00 na rana za a gama da Tinubu saboda gazawar da ya nuna a ofis
- Hon. Muhammad Gudaji Kazaureya ce ya gabatar da bincike kan kudaden da aka wawure, amma Tinubu ya yi biris, kuma ya cigaba da karbo bashi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kazaure, Jigawa - Tsohon ɗan majalisar tarayya daga jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure ya yi magana kan zaben 2027.
Hon. Gudaji Kazaure ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu inda ya ce ta lalata Najeriya gaba daya a kankanin lokaci.

Source: Facebook
Gudaji Kazaure ya sha alwashin kifar da Tinubu
Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa wanda ya karafe kafofin sadarwa.
Hon. Kazaure ya ce idan Allah ya kaimu zaben shekarar 2027, kafin 12:00 na rana an gama da Tinubu.
Kazaure ya ce yana da tabbacin haka saboda yadda Tinubu ya bata rawarsa da tsalle a dan lokacin da ya samu a kan karagar mulki a Najeriya.
Ya ce:
"Ina da tabbaci zuwa karfe 12:00 na rana, Asiwaju ya sha kasa wannan shi ne kwarin guiwarmu.
"Za mu yi adalci a wannan tafiya ta mu a Najeriya saboda sun riga sun kwafsa.
"Ka duba muna karbo bashin $22bn yayin da kuma muka san akwai kudi na gwamnati a hannun wasu."

Source: Facebook
Gudaji Kazaure ya zargi Tinubu na nakasa Najeriya
Hon. Kazaure ya ce abin takaici ne yadda ya kammala bincike kan wasu kudi da suka shafi almundahana amma Tinubu ya yi biris da haka.
Ya koka kan yadda ake ci gaba da karbo basuka duk da makudan kudi da wasu tsiraru suka sace suke yawo a cikin kasa.
2027: Shirin su Kazaure domin nakasa Tinubu
Tsohon dan majalisar ya ce a shirye suke domin tabbatar da an kayar da Tinubu tun da wuri a ranar zaben shugaban kasa.
Ya kara da cewa:
"Na ba shugaban kasa duka binciken da na yi da dukan takardu na fiye da N100trn maimakon ya gano kudin sai ya manta da lamarin.
"Amma duk da haka muna karbo bashi yayin wasu ke rike da tiriliyoyi a hannunsu.
"Sun lalata kasar nan kuma a shirye muke mu kwace mulki kuma za mu yi nasara idan Allah ya yarda."
Kazaure ya gana da Atiku kan zaben 2027
A baya, mun ba ku labarin cewa Alhaji Atiku Abubakar ya karɓi bakuncin Hon. Gudaji Kazaure, inda suka tattauna kan halin da Najeriya ke ciki da matakan da za a ɗauka a 2027.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɗin kan 'yan siyasa don ceto Najeriya, tare da samar da jagoranci da zai inganta rayuwar al’umma.
Gudaji Kazaure ya bayyana cewa sun shirya bin tsarin Atiku da shugabannin Arewa don samar da ci gaba da ceto Najeriya daga matsalolin da ta shiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

