Ana Shirya Yadda Za a Shigo Arewa a Kayar da Atiku, Kwankwaso da Wasu Jiga Jigai a 2027

Ana Shirya Yadda Za a Shigo Arewa a Kayar da Atiku, Kwankwaso da Wasu Jiga Jigai a 2027

  • Jam'iyyar PDP na ci gaba da ƙoƙarin dawo da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Mista Peter Obi zuwa inuwarta kafin zaɓen 2027
  • Farfesa Jerry Gana, ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa PDP ya hango nasarar da Peter Obi zai iya samu a Arewa idan ya nemi takara a jam'iyyar
  • Ya ce sun tuntuɓi Peter Obi kuma suna kan aikin lalubo manyan mutanen da za su iya ba mara ɗa kunya a babban zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana shirin da suke yi a jam'iyyar PDP na lashe ƙuri'un jihohin Arewa a zaɓen 2027.

Jerry Gana, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP a 1998, ya ce za su tsayar da ɗan takarar da zai kayar da duka ƴan siyasar Arewa irinsu Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

"Babu mai dakatar da mu," An shirya kawo wa Tinubu, APC miliyoyin ƙuri'u a Kano a 2027

Farfesa Jerry Gana.
Jigon PDP ya ce Peter Obi zai iya kayar da duka ƴan siyasar Arewa a zaɓen 2027 Hoto: @JerryGana
Asali: Twitter

Farfesa Gana ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na Arise TV a ranar Laraba, 30 ga wstan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi zai ba Atiku da Kwankwaso mamaki

Ya ce idan Peter Obi ya dawo PDP, zai kayar da kowane ɗan takara daga Arewacin Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wannan kalamai na Jerry Gana na zuwa ne yayin da jita-jita ke yawo kan yiwuwar dawowar Obi cikin jam’iyyar PDP, duk da ya haɗa kai da haɗaka, ADC.

Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin LP a zaɓen 2023, ya fice daga PDP a watan Mayu 2022 domin ya cimma burinsa a inuwar LP.

Farfesa Gana ya ce:

“PDP na nan da ranta a jihohin Arewa, idan Peter Obi ya tsaya takara a PDP, zai doke kowane ɗan takara saboda mutanenmu masu adalci ne kuma masu gaskiya.”

Kara karanta wannan

ADC ta yi bayani kan rashin sauya sheƙar El Rufa'i da Obi har yanzu

PDP ta fara shirin dawo da Peter Obi

Ya ƙara da cewa tuni PDP ta fara tuntubar Peter Obi domin tattaunawa kan yadda zai dawo jam'iyyar kafin zaɓen 2027, rahoton Vanguard.

“Mun tuntuɓi Peter Obi saboda ni ke jagorantar tawagar bincike, muna nazari kan wasu mutane da karɓuwarsu a wurin jama'a. Peter Obi na cikinsu amma mai yiwuwa akwai wanda ya fi shi," in ji Gana.
Farfesa Jerry Gana da Peter Obi.
PDP na ci gaba da zawarcin Peter Obi gabanin zaɓen 2027 Hoto: @RealJerryGana, @PeterObi
Asali: Twitter

Jerry Gana ya kuma amince cewa PDP ta yi kuskure wajen barin Obi ya fice daga jam’iyyar kafin zaɓen 2023.

“Mun yi kuskure a 2023. Da ni ne Atiku, da na ce masa: ‘Peter, yanzu lokacinka ne; zan ba ka mataimakin shugaban ƙasa,’ amma bai yi hakan ba,” in ji shi.

Game da rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi a yanzu, Gana ya ce matsalar ta taƙaitu ne kawai kan wasu ‘yan ƙalilan daga cikin shugabanni da ke Abuja, ba ta shafi mambobin ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta ɓarke a haɗakar su Atiku, jigon ADC ya naɗa kansa shugabanci

PDP ta miƙa tikitin takararta zuwa Kudu

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP ta amince da ɗauko ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu a zaben 2027.

A cewarta, wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen dawo da ainihin manufofin jam’iyyar PDP na adalci, daidaito da haɗin kan ƙasa.

Farfesa Jerry Gana, tsohon Ministan Yaɗa Labarai kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP, ya tabbatar da wannna matsaya da suka cimma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262