Sunan Kwankwaso Ya Fito: Malami Ya Samu Wahayin Wanda Zai Yi Wa Madugu Mataimaki

Sunan Kwankwaso Ya Fito: Malami Ya Samu Wahayin Wanda Zai Yi Wa Madugu Mataimaki

  • Wani sanannen Fasto a jihar Akwa Ibom ya yi hasashen abin da ya gano a mafarki game da siyasar 2027 da sabon shugaban kasa
  • Fasto Francis Udo ya ce Allah ya nuna masa Rabiu Musa Kwankwaso zai gaji Bola Tinubu, bayan mulkin ya koma Arewa a 2031
  • Udo ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio zai kasance mataimakin shugaban kasa a tikitin Kwankwaso

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Sanannen Fasto kuma shugaban 'Prayer Foundation Network', Francis Udo, ya bayyana hasashen siyasar Najeriya da Akwa Ibom.

Malami kuma limamin na mabiya addinin kirista ya fadi abin da zai faru bayan karewar wa'adin Shugaba Bola Tinubu a Mayun shekarar 2031.

An kira sunan Kwankwaso da cewa zai gaji kujerar Tinubu
Malami ya hango Kwankwaso a matsayin shugaban kasa. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Fasto ya gano mataimakin Kwankwaso bayan Tinubu

Malamin ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Punch a birnin Uyo ranar Laraba 30 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

'A taimaka masa kamar Buhari': An roƙawa Tinubu alfarma wurin ƴan Arewa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Udo ya ce Allah ya nuna masa a mafarki cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai gaji Tinubu bayan mulki ya koma Arewa a 2031.

A cewarsa:

“Shugaban majalisar dattawa na yanzu, Sanata Godswill Akpabio, kamar yadda Allah ya nuna mani, zai kasance mataimakin Kwankwaso a zaben shugaban kasa.
"Kwankwaso zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inda zai fara takarar mataimakin shugaban kasa tare da Tinubu, kafin daga baya ya tsaya takarar shugaban kasa kuma ya samu nasara.
”A mafarkin da Allah ya nuna mani, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa yanzu, Femi Gbajabiamila, zai zama shugaban majalisar dattawa mai zuwa, yayin da Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, zai zama Sakataren Gwamnatin Tarayya.”
Sunan Akpabio ya fito a matsayin mataimakin shugaban kasa
Malami ya hango Akpabio zai zama mataimakin Kwankwaso bayan Tinubu. Hoto: Godswill Akpabio.
Source: Facebook

Akwa Ibom: Fasto ya yi hasashen sabon gwamna

Malamin ya kuma bayyana yadda siyasar jihar Akwa Ibom za ta kasance bayan wa’adin gwamna Umo Eno na biyu, inda ya ce Eno zai zama sanata mai wakiltar mazabar Uyo (Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas).

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya kare shugaban kasa, ya fadi dalilin da ya sa ake adawa da shi

Ya ce gwamna Eno zai samu sabani da Sakataren Gwamnatin Jiha na yanzu, Prince Enobong Uwah, domin dukkansu za su nemi kujerar sanata daga mazabar Uyo, amma daga baya za a warware matsalar.

Uwah zai zama mataimakin gwamna na Obongemem Ekperikpe Ekpo, wanda shi ne Ministan Man Fetur (Iskar Gas), wanda kuma Allah ya nuna masa zai zama gwamnan jihar a 2031.

“Ekperikpe Ekpo, Ministan Harkokin Man Fetur (Iskar Gas), Allah ya nuna mani, shi ne zai zama Gwamnan Akwa Ibom a 2031 bayan mulki ya koma yankin Ikot Ekpene.
“Zai samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jiha na yanzu, Prince Enobong Uwah, a matsayin mataimakinsa; ku rubuta, wannan shi ne abin da Allah ya nuna min."

- Cewar Fasto Udo

Fasto ya magantu kan masu takara a 2027

Mun ba ku labarin cewa Fasto Elijah Ayodele ya yi magana kan waɗanda za su tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Ayodele ya ce takarar shugaban kasa ta 2027 za ta kasance tsakanin Bola Tinubu da wasu mutane biyu da aka nuna masa.

Ya gargadi Peter Obi ka da ya tsaya takara, domin yin hakan zai sauƙaƙa wa Tinubu samun wa'adi na biyu a zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.