Bayan Saɓani Ya Shiga tsakani, Shugaba Tinubu Ya Gana da na Hannun Daman Kwankwaso

Bayan Saɓani Ya Shiga tsakani, Shugaba Tinubu Ya Gana da na Hannun Daman Kwankwaso

  • A ƴan kwanakin nan, fadar shugaban kasa ta yi magana kan jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a lokuta daban-daban
  • Hakan ya biyo bayan sukar da tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso ya yiwa gwamnatin Bola Tinubu, inda ya ce tana fifita Kudu kan Arewa
  • Sai dai a yau Laraba, ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin na hannun daman Kwankwaso ne, Hon. Abdulmumin Kofa ya gana da Tinubu a sirrance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya gana da Hon. Abdulmumin Jibrin, ɗaya daga cikin abokan siyasa na jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hon. Abdulmumini, wanda ke wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga jihar Kano ya ziyarci Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yau Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya ari bakin gwamnoni kan tazarcen Tinubu a 2027

Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa da shugaban kasa.
Shugaba Tinubu ya gana da Abdulmumini Kofa a Aso Rock Hoto: @AbdulAbmj
Source: Twitter

Ɗan Majalisar Tarayya na daga cikin masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulmumini Kofa ya amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan ganawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Abdulmumini Kofa na shirin shiga APC?

Da aka tambaye shi ko yana shirin komawa APC ne, ɗan Majalisar ya bayar da amsa a natse, yana mai cewa ba abin da ba zai iya faruwa ba.

"Ina ga lokacin wannan batun bai yi ba, amma dai komai na iya faruwa. Abu mafi muhimmanci shi ne zaman lafiya da haɗin kan ƙasar nan. Kuma na yi imani cewa idan muka kai ga gabar, za mu tsallaka.”

Dan majalisar ya ce ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da abokantaka mai tsawo tsakanin Tinubu da Kwankwaso.

Meyasa Kofa ya ziyarci Shugaba Tinubu?

“Na zo ne domin ganin Shugaban Ƙasa, kuma kamar yadda aka sani, akwai alaƙa tsakanin Tinubu da jagoranmu na NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Sukar gwamnati: Jam'iyyar NNPP ta ba Tinubu shawara kan Kwankwaso

"Saboda haka, ban ga abin mamaki ba dan na zo gaida shi, na duba lafiyarsa, da kuma tattauna wasu batutuwan ƙasa da nake ganin suna da amfani ga al’ummar Najeriya.”

- Abdulmumini Kofa.

Kofa ya taɓo alaƙar Ƙwankwaso da Tinubu

Da aka tambaye shi ko ziyarar tasa tana da nasaba da wani yunkurin sulhu tsakanin Kwankwaos da fadar shugaban ƙasa, Jibrin ya ce dukkan shugabannin biyu suna da kishin ci gaban ƙasa duk da suna da banbancin ra'ayi.

A baya-bayan nan, Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita yankin Kudu a rabon ayyukan ababen more rayuwa.

Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa.
Hon. Abdulmumini Kofa ya ce ba abin da ba zai iya faruwa ba game da batun komawa APC Hoto: Hon. Abdulmumini Kofa
Source: Facebook

A rahoton The Cable, Abdulmumini Jibrin ya ce:

“To, dukkansu manyan ‘yan siyasa ne, Shugaban Ƙasa babban ɗan siyasa ne, haka jagoranmu na NNPP, ina da yakinin cewa suna da kishin zaman lafiya, haɗin kai da cigaban Najeriya.."

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da ganawar Hon. Kofa da shugaba Tinubu a wani bidiyo da Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X.

Kwankwaso ya bugi ƙirji kan masoyansa a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce babu wanda zai iya kayar da Kwankwasiyya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Labarin ƙarya," An ji gaskiyar abin da ya faru kan batun ganawar Tinubu da Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana cewa duk wani ɗan siyasa da ke tafiya da akidar Kwankwasiyya zai samu goyon bayan jama'a a ko'ina ya tsinci kansa.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga gwamnoni da su bunƙasa fannonin ilimi da sauran ayyukan inganta walwalar al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262