Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ɗauki Zafi kan Zargin Yiwa Ƙusa a ADC Tayin Kujerun Ministoci

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ɗauki Zafi kan Zargin Yiwa Ƙusa a ADC Tayin Kujerun Ministoci

  • Fadar shugaban 'kasa ta ce babu wani jami’in gwamnati da ke da ikon bayar da kujerun ministoci face shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Wannan na zuwa a matsayin martani ga kalaman tsohon shugaban ADC, Ralph Nwosu da ya yi cewa an yi masa tayin kujerun Ministoci
  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce a ce idan da gaske ne an yi masa tayin, ya kamata ya fadi sunaye da mukaman jami'an

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin da tsohon shugaban ADC, Mista Ralph Nwosu ya yi kan wasu manyan jami’an gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Nwosu, ya yi zargin cewa wasu manyan jami’an gwamnatin Tinubu sun yi masa alkawarin kujerun ministoci guda uku domin kada ya mika jam’iyyarsa ga haɗakar 'yan adawa

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ADC ya fadi yadda APC ta so rusa hadaka da raba mukaman minista

Hadimin shugaban kasa, Bwala tare da Tinubu
Fadar Shugaban kasa ta karyata ikirarin jagora a ADC Hoto: Daniel Bwala
Source: Twitter

A sanarwar da hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana wannan zargi a matsayin ƙarya da yaudara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin fadar shugaban kasa ga Ralph Nwosu

Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana cewa babu wani jami’i a gwamnatin Tinubu da ke da ikon yin irin wannan alkawari.

Ya ce:

“Babu wani jami’in gwamnati, komai girma da matsayinsa, da zai iya yin alkawari ko bayar da kujerar minista. Wannan iko ne da ke hannun shugaban ƙasa.”

Bwala ya ƙara jaddada cewa idan za a yi irin wannan muhimmiyar magana ta siyasa, sai ta fito daga bakin Shugaba Bola Tinubu kai tsaye, ba ta bakin wasu wakilai ko hadimai ba.

Hadimin Tinubu ya ƙalubalanci Nwosu

Daniel Bwala ya bukaci Uche Nwosu ya bayyana sunaye da mukaman waɗanda ya ce sun yi masa wannan alkawari saboda dakatar da shi daga mika ADC ga 'yan adawa.

Jiga-jigan ADC, jim kadan da mika jam'iyya ga hadakar adawa
Fadar Shugaban kasa ta nemi shaida kan ikirarin Nwosu Hoto: ADC Coalition 2027
Source: Facebook

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

“Yadda ya iya fito wa tare da yin zargin cewa an yi masa tayin mukamai, ya kamata ya fadi sunayensu da matsayinsu. Idan ba haka ba, to wannan zargi ba shi da tushe.”

Ya yi zargin cewa fadin karairayi irin wannan a siyasar Najeriya na nuna rauni da ake da shi wajen tabbatar da dimokuradiyya a 'kasar.

An yi martani ga hadimin Tinubu

Al’umma da dama sun tofa albarkacin bakinsu a dandalin X kan wannan batu, inda wasu ke

@MichalDammy ya ce:

“Kila kai ba ka san cewa Tinubu ya aiki wani zuwa wajensa ba. Ba za ka iya sanin duk wani mataki da Tinubu ke ɗauka ba. APC da Tinubu ba su da amana.”

@Naijatvv ya rubuta:

“Wanda suka san Mista Nwosu da gaske, sun san cewa ƙarya na daya daga cikin abubuwan da iya. Mutumin da ya karɓi kudi ya sayar da jam’iyyarsa, yanzu yana ikirarin an ba shi kujerar minista.”

Zargin Nwosu a kan gwamnatin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Ralph Nwosu, ya ce wasu daga cikin jami’an gwamnatin Bola Tinubu sun so su yi katsalandan a hadakar adawa.

Kara karanta wannan

Super Falcons: Yadda Tinubu ya shiga fargabar hawan jini a fadar shugaban kasa

A cewarsa, jami’an sun ba shi tayin kujerun ministoci guda uku: Daya zai karɓa da kansa, yayin da zai iya ba sauran biyun duk wanda ya ga dama domin hana hadakar ta shiga ADC.

A kwanakin baya, Nwosu ya mika shugabancin jam’iyyar ADC ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, wanda yanzu ke matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng