Uba Sani Ya Faɗi Abin da Tinubu Yake Yi da ba a Taɓa Shugaban Ƙasa da Ya Yi ba
- Gwamna Uba Sani ya yabawa Bola Tinubu saboda irin gudunmawar da ya ce yake ba gwamnoni a Najeriya baki daya
- Uba Sani ya ce babu wani shugaban kasa da ya tallafa wa gwamnoni kamar yadda Tinubu ke yi a yanzu wanda ya yi fice
- Ya bayyana hakan ne a taron kwanaki biyu da Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna don inganta hulɗar gwamnati da jama’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yabawa Bola Tinubu kan irin kokari da yake yi a Najeriya tun bayan hawansa kujerar mulki.
Mai girma Uba Sani ya ce babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da ya tallafa wa gwamnoni kamar Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
An yi taron duba ayyukan Tinubu a shekaru 2
Yayin bude taron kwanaki biyu kan hulɗar gwamnati da ‘yan ƙasa, Uba Sani ya ce gwamnoni ba za su iya adawa da Tinubu ba, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganganun gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnoni da dama ciki har da na jam’iyyun adawa ke goyon bayan Shugaba Tinubu.
Taron wanda Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya, ya gudana a 'Arewa House' Kaduna tare da mahalarta daga gwamnati da ƙungiyoyi.
Taken taron shi ne:
“Binciken Alkawuran Zaɓe: Haɓaka Hulɗar Gwamnati da Jama’a don Haɗin Kan Ƙasa.”
Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, kungiyoyin fararen hula da masu tsara manufofi don tattauna gaskiya da ingancin ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Abin da Uba Sani ya ce game da Tinubu
Shugaba Tinubu ya samu wakilcin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da Ministan Watsa Labarai da Tsare-tsare, Mohammed Idris.
A cewar Uba Sani:
“Babu wani shugaban Najeriya da ya tallafa wa gwamnoni da jihohi kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi yanzu.”
Ya ce saboda hakan, ba zai yiwu wani gwamna a Najeriya ya yi wa Shugaba Tinubu adawa ba a halin yanzu.
Uba Sani ya fadi kokarin Tinubu a Arewa
Gwamnan ya bayyana cewa karo na farko a tarihin Najeriya ne gwamnatin Tarayya ke shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Arewa.
Ya ce wannan tsari na daban yana nuna yadda gwamnati ke sauya hanyoyin magance matsalolin ƙasa da ci gaban yankuna, cewar Tribune.
Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello dai ƙungiya ba ta siyasa da addini ba, wacce aka kafa a shekarar 2009 domin girmama marigayi Sir Ahmadu Bello.
Uba Sani ya ce Tinubu zai zarce s 2027
Kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabo batun yiwuwar sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027 da ake tunkara.
Uba Sani ya bayyana cewa babu wani gwamna daga cikin gwamnonin Najeriya da zai yi adawa da tazarcen mai girma Bola Tinubu duba da ayyukan alheri da ya ke yi.
Gwamnan ya nuna cewa gwamnonin za su rama biki ne kan irin goyon bayan da shugaban kasan ya ba su tun bayan hawansa kujerar mulki a Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng

