Tsohon Shugaban ADC Ta Fadi Yadda APC Ta so Rusa Hadaka da Raba Mukaman Minista

Tsohon Shugaban ADC Ta Fadi Yadda APC Ta so Rusa Hadaka da Raba Mukaman Minista

  • Tsohon shugaban jam’iyyar ADC ya ce wasu jami’an gwamnati sun ce zai samu mukaman minista har uku idan ya shiga hadaka
  • Jam’iyyar ADC ta mika ragamar shugabanci ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark domin kulla hadakar 'yan adawa
  • Rahotanni sun nuna cewa Ralph Nwosu ya ce hukumar INEC ta tura jami’anta bakwai don saka idanu kan taron NEC na jam’iyyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu ya bayyana cewa wasu jami’an gwamnatin Bola Tinubu sun nemi ya fasa amfani da jam’iyyar a matsayin dandalin hadaka.

A cewarsa, an ce zai samu mukaman minista uku a nan gaba, daya ya karɓa, sauran biyun kuma ya bai wa wanda ya ga dama.

Kara karanta wannan

"Ba don Tinubu ba ne": Atiku ya fadi manufar kafa hadakar 'yan adawa a ADC

Tsohon shugaban ADC na kasa, Ralph Nwosu
Tsohon shugaban ADC na kasa, Ralph Nwosu tare da David Mark. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Rahoton Arise News ya nuna cewa Nwosu ya ce duk da haka, bai amince ba domin kare dimokuradiyya da makomar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya ne Ralph Nwosu ya mika shugabancin jam’iyyar ga tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban rikon kwarya.

Nwosu ya ce APC ta masa tayin ministoci

Nwosu ya bayyana cewa wasu mutane daga cikin gwamnatin APC sun nemi su dakile hadakar 'yan adawa ta hanyar yi masa tayin mukaman minista har uku a nan gaba.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

"Sun ce zan karɓi mukami daya, sai in bai wa wasu biyun. Amma na ki, domin Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya guda ba bayan mun dage wajen korar sojoji daga mulki."

Ya ci gaba da cewa:

"Mun zabi kare dimokuradiyya da makomar ƙasar nan. Jama’a sun gaji da mulkin jam’iyyar da ke kan karagar gwamnati yanzu."

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro Tinubu a APC, tsofaffin mambobin ANPP sun aika da gargadi

INEC ta saka idanu a taron ADC

Taron NEC da ya tabbatar da mika shugabanci ga David Mark ya samu sa ido daga jami’ai 7 na hukumar zabe ta kasa (INEC), a matsayin hukumar da ke lura da harkokin jam’iyyu a Najeriya.

Nwosu ya bayyana cewa dukkan mambobin NEC da na kwamitin zartarwa sun amince da sauka daga mukamansu domin ba sababbin shugabanni damar tafiyar da jam’iyyar cikin sabon salo.

Atiku da sauran 'yan siyasa yayin taron ADC a Abuja
Atiku da sauran 'yan siyasa yayin taron ADC a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

'ADC na samun karbuwa a Najeriya' - Nwosu

Nwosu ya ce, bayan kafa kawancen, jam’iyyar ADC ta karɓi sababbin mambobi fiye da miliyan 3 cikin mako biyu.

A cewarsa:

"ADC ta kasance karamar jam'iyya, amma yanzu ita ce jam’iyyar da ke gaba da sauran jam’iyyu wajen samun karbuwa.
"Jama’a sun nuna kin amincewa da salon tafiyar gwamnati mai ci."

Ya jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da jagorantar kawancen jam’iyyu domin ceto dimokuradiyya da kare muradun ‘yan Najeriya.

Akume ya bukaci marawa Tinubu baya

A wani rahoton, kun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya bukaci 'yan Arewa su mara wa Bola Tinubu baya.

Kara karanta wannan

ADC: Sanata a PDP ya ayyana Atiku a matsayin jagoran siyasar Arewa

George Akume ya ce bai kamata 'yan Arewa su shiga wata tafiya da za ta kawo cikas kan ayyukan alheri da Bola Tinubu ya fara ba.

Akume ya yi kira ga duk wani dan Arewa da ke son tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 da ya hakura har sai shekarar 2031.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng