2027: Ana Lallaba Atiku da Sauran 'Yan Arewa Su Hakura sai Tinubu Ya Yi Tazarce
- Sakataren gwamnatin tarayya ya bukaci ’yan siyasa daga Arewacin Najeriya su hakura da batun takara a 2027, su jira 2031
- George Akume ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi adalci wajen raba mukamai da cigaban Arewacin Najeriya
- Baya ga haka, Akume ya ja hankalin ’yan siyasa da kada su shiga rukunin da za su kawo cikas kan ayyukan da aka fara a yanzu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya shawarci ’yan siyasar Arewacin Najeriya da su hakura da batun takarar shugaban kasa a 2027.
Akume ya bayyana cewa ya kamata su jira har sai bayan wa’adin Shugaba Bola Tinubu na biyu ya kare a 2031.

Source: Twitter
Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Akume ya bayyana haka ne a wani taron kwana biyu da ake yi a Kaduna domin bayyana nasarorin Tinubu.

Kara karanta wannan
Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu
'Tinubu ya ba Arewa kulawa,' Akume
Akume ya yi watsi da rade-radin da ke cewa Arewa ba ta samu kulawa daga gwamnatin Tinubu ba, yana mai jaddada cewa an ba mutane da dama daga yankin a muhimman mukamai.
Ya ce:
“Maganar cewa ba a damawa da Arewa karya ce. Idan aka duba aikin titin Sokoto zuwa Bagary, ya fi tsawon na Lagos zuwa Calabar.”
Haka zalika, ya ce gwamnatin Tinubu ta bunkasa tsaro da noma, inda hakan ya taimaka wajen rage farashin kayan abinci da bunkasa isasshen abinci a kasar.
Akume ya kare Tinubu kan tallafin mai
Akume ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya kara habaka kudin da ake ba gwamnoni don aiwatar da muhimman ayyuka.
Ya ce hakan ne ya bai wa jihohi damar gudanar da manyan ayyukan raya kasa tare da kawo romon dimokiradiyya ga jama’a.
Nasarorin da Tinubu ya samu - Akume
Sanata Akume ya jaddada cewa a cikin shekara biyu da wata biyu kacal, gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a fannonin diflomasiya, tsaro, noma, ilimi, tsarin haraji da yaki da cin hanci.
Ya kara da cewa:
“Shugaba Tinubu ya gina tubalin sabuwar Najeriya ta hanyar jagoranci mai hangen nesa da jajircewa ga ci gaban kasa.”
Ya ce bisa la’akari da irin nasarorin da aka samu, ya kamata ’yan siyasa daga Arewa su jingine burinsu na 2027, su bai wa shugaban kasa damar kammala aikinsa.

Source: Twitter
An roki ’yan siyasa su guji tayar da rikici
A karshe, Akume ya gargadi ’yan siyasa da su guji shiga kungiyoyin da za su hana ci gaban da Tinubu ya assasa, yana mai cewa shugaba Tinubu ya taba rayuwar kowane bangare na kasa.
Rahoton VON ya tabbatar da cewa ya ce:
“'Yan siyasa masu kishi su hakura zuwa 2031. Kada ku hana cigaba da shugaba Tinubu ya fara. Yana tafiya tare da kowa.”
Gwamna Inuwa ya ce suna tare da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Bola Tinubu ya taka rawar gani.
Inuwa Yahaya ya ce shugaban kasar ya cika da dama daga cikin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
Ya bayyana cewa lura da alkawuran da Bola Tinubu ya cika, za su goyi bayan shugaban kasar domin samun wa'adi na biyu a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

