Adamu Garba Ya Tunawa Ƴan Najeriya Abin da Suka Manta tun Buhari na Raye a 2015
- Adamu Garba II ya tuna yadda tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari ya karɓi Najeriya komai ya taɓarɓare a 2015
- Matashin da ya nemi tikitin shugaban ƙasa ya ce APC ta yi matuƙar koƙari idan aka kwatanta da yadda ta gaji kasar nan a baya
- Adamu ya ce Shugaba Buhari ya yi ƙoƙari matuka a zamanin mulkinsa, yanzu kuma Bola Ahmed Tinubu ya ɗora daga wurin da ya tsaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon ɗan takara da ya nemi tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Adamu Garba ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta karɓi Najeriya a birkice a 2015.
Idan baku manta ba bayan shekara 16 a mulki, jam’iyyar PDP ta sha kaye a hannun APC a babban zaben 2015.

Asali: Twitter
Premium Times ta rahoto cewa tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan ya sha kaye a hannun marigayi Muhammadu Buhari na APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu ya tuna yadda Buhari ya karɓi Najeriya
Sai dai a yayin wata hira da tashar AIT a shirin Focus Nigeria, Adamu Garba, wanda ya nemi tikitin APC a 2023, ya ce jam’iyyarsu ta karɓi mulki ne a lokacin da Najeriya ta kai gargara.
“Duk wasu kayan aiki sun lalace a lokacin da APC ta zo. Muna da ginshikai huɗu, diflomasiyya, leƙen asiri, sojoji, da tattalin arziki, duka an yi kaca-kaca da su. Shi ya sa ƴan ta'adda suka mamaye ƙasarmu,” in ji shi.
Ya ce a lokacin da Boko Haram, 'yan fashi da makami, da kuma haramtacciyar ƙungiyar IPOB, wadda shugaban ta Nnamdi Kanu ke fuskantar shari’a kan zargin ta’addanci, sun mamaye Najeriya.
Wani namijin ƙoƙari Buhari ya yi a mulkinsa?
Duk da harin da 'yan fashin daji ke kaiwa jami'an tsaro a Arewacin ƙasar, Garba ya yabawa gwamnatin APC, yana cewa an riga an ci galaba kan Boko Haram da 'yan fashi.

Kara karanta wannan
Tinubu: An yi hasashen wanda zai zo na 1, na 2, na 3 da na 4 a zaɓen shugaban ƙasar 2027
“Yanzu da nake magana da ku, babu ko yanki guda a hannun Boko Haram. Ko ‘yan bindiga da suka ƙaru a wa’adin farko na Buhari, yanzu NSA ya yi nasarar kawar da su,” inji shi.
Adamu Garba ya yi fatali da duk wata ƙididdiga da ya kira ta bogi da ake nuna cewa tattalin arziki ya fi zama da gindinsa a lokacin mulkin PDP.

Asali: Facebook
Adamu Garba ya yabawa gwamnatin APC
“APC ta zo da gaskiya, ta fasa wannan ƙwallon da ake ganin yana ƙyalli amma babu komai a ciki. Don haka, dole ne a sake fasalin tattalin arziki.”
“Shugaba Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa, amma bai samu damar kafa tushen tattalin arziki ba. Ya fi maida hankali ne kan harkar tsaro kuma ya yi kokari sosai.”
"Shugaba Bola Tinubu ya ce a'a, zai yi abin da kowa ke tsorata da shi. Zai cire tallafin mai gaba ɗaya, sannan ya saki Naira domin a san ainihin darajar ta."

Kara karanta wannan
Bayan tafiyar Atiku, an yi hasashen matsayi da PDP za ta ƙare a sakamakon zaɓen 2027
- Adamu Garba.
Shugaba Tinubu ya ja hankalin gwamnoni
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jam'iyyarsa ta APC da su zage damtse, sun dage wajen kawo ci gaba ga mutanen da ke ƙarƙashinsu.
Ya yi ikirarin cewa har yanzu ƴan Najeriya da dama ba su gamsu da yadda ake tafiyar da mulki da sanin amfanin romon dimokuraɗiyya ba.
Tinubu ya buƙaci shugabannin jam’iyya da ƴan siyasa da aka zaɓa da su sake kusantar jama’a tare da ƙara himma wajen kyautata rayuwar al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng