Gwamna Uba Sani Ya Ari Bakin Gwamnoni kan Tazarcen Tinubu a 2027

Gwamna Uba Sani Ya Ari Bakin Gwamnoni kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabo batun yiwuwar sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027
  • Uba Sani ya bayyana cewa babu wani gwamna daga cikin gwamnonin Najeriya da zai yi adawa da tazarcen mai girma Bola Tinubu
  • Gwamnan ya nuna cewa gwamnonin za su rama biki ne kan irin goyon bayan da shugaban kasan ya ba su tun bayan hawansa kujerar mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Gwamna Uba Sani ya ce zai kasance da wuya a samu wani gwamna a Najeriya da zai ƙalubalanci sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Uba Sani ya tabo batun tazarcen Tinubu
Gwamna Uba Sani ya ce gwamnoni za su goyi bayan tazarcen Tinubu Hoto: @ubasanius, @DOlusegun
Source: Twitter

An bude muhimmin taro a Kaduna

Gwamna Uba Sani ya yi wannan bayani ne yayin buɗe taron tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan kasa na kwanaki biyu a Kaduna, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

2027: Malamin addini ya hango kujerar gwamnoni 7 da ke fuskantar barazana

Gidauniyar Ahmadu Bello Memorial Foundation (SABMF) ce ta shirya taron a Arewa House, da ke Kaduna.

SABMF wata gidauniya ce maras alaƙa da siyasa ko addini, wadda aka kafa a shekarar 2009 domin girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

Shugaba Tinubu ya samu wakilcin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, da kuma ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris.

Gwamna Uba Sani ya yabi Shugaba Tinubu

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ba gwamnonin jihohi goyon bayan da ya dace.

"Baya ga haka, babu wani shugaban ƙasa a tarihin Najeriya da ya ba wa gwamnoni da gwamnatocin jihohi goyon baya kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi yanzu."
"Saboda haka, da wuya a ce wani gwamna a Najeriya zai bijire wa shugaban kasa."

- Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakan tattaunawa da kungiyoyin da ba na gwamnati ba a Arewacin Najeriya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rikita jiga jigan APC a taro, ya taka rawa a waƙar 'Omologo' ta Rarara

Uba Sani ya yabi Shugaba Tinubu
Gwamna Uba Sani ya yi magana kan tazarcen Tinubu a 2027 Hoto: @ubasanius
Source: Facebook
"A karon farko a tarihin Najeriya, gwamnati na tattaunawa da kungiyoyin da ba na gwamnati ba domin duba ci gaban yankin Arewa da fahimtar halin da ake ciki."
"Wannan sabon salo da ba a taɓa gani ba yana nuna yadda ake sauya tsarin warware matsalolin ƙasa."

- Gwamna Uba Sani

Shugaba Bola Tinubu dai har yanzu bai fito ya bayyana cewa zai sake neman takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba.

Sai dai, shugaban kasa ya samu goyon baya daga wajen manyan 'yan siyasa a ciki da wajen jam'iyyar APC kan yin tazarce a 2027.

Ba abun mamaki ba ne

Wani mazaunin Katsina, Abba Tukur Saleh ya shaidawa Legit Hausa cewa ba abin mamaki ba ne don gwamnan ya yi wadannan kalamai.

"Su gwamnoni ai kakarsu ta yanke saka a gwamnatin Tinubu. Ai dole su so ya ci gaba da mulki."
"Ba su damu da wahalar da ake sha ba sakamakon manufofin da gwamnatin ke aiwatarwa tun da su an kara musu kudaden da suke samu duk.wata daga asusun tarayya."

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar ATT ta samo mafita ga Arewa kan tazarcen Shugaba Tinubu

- Abba Tukur Saleh

'Yan ANPP sun gargadi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsofaffin mambobin jam'iyyar ANPP sun aika da sakon gargadi ga shugaban kasa Bola Tinubu, kan ci gaba da zamansu a APC.

Mambobin na ANPP sun yi gargadin cewa za su fice daga APC idan har Shugaba Tinubu ya kwace kujerar mataimakin shugaban kasa daga bangarensu.

Hakazalika sun koka kan yadda aka maida su saniyar ware a cikin gwamnatin Muhammadu Buhari da Tinubu duk kuwa da irin gudunmawar da suka ba da wajen kafa jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng