2027: Babachir Lawal Ya Fadi Gagarumin Kalubalen da ke Tunkaro Gwamnonin Arewa

2027: Babachir Lawal Ya Fadi Gagarumin Kalubalen da ke Tunkaro Gwamnonin Arewa

  • Tsohon Sakataren gwamnati, Babachir Lawal ya ce 'yan siyasar Arewa da ke neman takara a zaben 2027 da ke karatowa na cikin matsala
  • Ya ce matukar suna zaune a jam'iyya mau mulki ta APC, ba su da bakin da za su nemi jama'a su zabe su duba da illar da aka yi ga Arewa
  • Babachir Lawal ya kara da cewa yanzu haka, ADC na ci gaba da tattauna wa da wasu daga cikin gwamnoni a Arewa domin sauya sheka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa akwai babbar matsala da ke fuskantar dukkan shugabannin siyasa a Arewa.

Ya bayyana cewa za a samu gagarumar matsala a babban zaben 2027 da ke karato wa, matukar ba su dauki matakin gyara ba.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan APC ya fadi shirin da suke yi kan hadakar 'yan adawa

Tsohon sakataren gwamnati, Babachir Lawal
Babachir Lawal ya ce akwai matsala ga 'yan siyasar Arewa Hoto: Babachir Lawal
Source: Facebook

Jaridar Vanguard News ta wallafa Babachir ya ce jam’iyyar APC ta lalata Arewa kuma ta ware yankin, don haka babu wanda zai iya yakin neman zaɓe a Arewa cikin jam’iyyar mai mulki.

Shawarar Babachir ga gwamnonin Arewa

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Babachir ya bayyana cewa gwamnonin Arewa da ke shirin neman wa’adi na biyu ba za su samu nasara ba, sai sun fice daga APC su koma jam’iyyar ADC ba.

Tsohon SGF ya ce jam’iyyar adawa ta ADC tuni ta fara tattaunawa da wasu daga cikin gwamnonin Arewa, domin janyo su gabanin zaɓen 2027.

Babachir Lawal ya ce:

“Sai sun koma ADC ne za su ci zaɓe."
“Wane ɗan siyasar Arewa zai iya fita ya yi yakin neman zaɓe da sunan APC a wannan karo? Babu. Sai dai tun da farko ba ka da niyyar yin nasara.”

Babachir ya goyi bayan Kwankwaso

Babachir Lawal ya bayyana goyon bayansa ga sukar da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi wa gwamnatin Tinubu, musamman dangane da watsi da yankin Arewa a fannin ayyukan raya ƙasa.

Kara karanta wannan

Ana sa ran zai bar NNPP, Kwankwaso ya bada kafa da ya karbi 'yan APC a Kano

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Babachir Lawal ya goyi bayan Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Duk wani ɗan Najeriya da ke da alaƙa da Arewa ya san babu wani aikin raya ƙasa da ake yi a wannan yankin."

Ya bayyana cewa babu wani abin a zo da gani da gwamnatin nan za ta bugi kirji ta ce ana gudanar da shi yadda ya kamata a Arewacin kasar nan.

Babachir Lawal ya fice daga APC

A baya, mun wallafa cewa Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, Babachir David Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance.

Ficewar tasa na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta da kansa, wadda ya aika zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na gundumar Banshika, da ke ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da kwanan wata 29 ga Yuni, 2025, Babachir Lawal ya bayyana cewa ficewar sa daga jam’iyyar ta fara aiki daga lokacin rubuta wasiƙar, ba tare da wani jinkiri ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng