Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa, An Zarge Shi da Yunkurin Tunzura Ƴan Arewa

Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa, An Zarge Shi da Yunkurin Tunzura Ƴan Arewa

  • Jigon jam'iyyar APC, Yekini Nabena ya soki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Nabena ya bayyana cewa Kwankwaso ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da watsi da Arewa saboda neman ƙarin farin jini kafin zaɓen 2027
  • Ya ce sun riga sun gano wasan siyasa da Kwankwaso ke bugawa, yana mai cewa ƴan Arewa ba za su aminta da shi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Honarabul Yekini Nabena, ya tsoma baki kan zargin da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya yi kan gwamnatin Tinubu.

Nabena bayyana rashin jin daɗinsa kan kalaman da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi cewa gwamnati mai ci ta yi watsi da Arewa.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hango kuskuren da Kwankwaso ya yi a kalamansa kan Arewa

Tsohon kakakin APC da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso.
An zargi Kwankwaso da yunƙurin tunzura ƴan Arewa kafin zaben 2027 Hoto: @officialAPCNig, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tribune Nigeria ta ce tun farko Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da fifita yankin Kudu wajen rabon ayyuka da gina tituna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kano ya yi zargin cewa wannan gwamnati ta yi watsi da yankin Arewa, ta maida hankali wajen gina Kudu, yankin da shugaban ƙasa ya fito.

An zargi Kwankwaso da shirin tunzura Arewa

Amma a martaninsa kan waɗannan kalamai, Honarabul Nabena ya zargi Kwankwaso da ƙoƙarin tunzura masu kaɗa ƙuri’a a Arewa don ƙara farin jini kafin zaɓen 2027.

Ya ce irin wannan dabarar ta “kasuwancin siyasa” da wasu ‘yan siyasa suka yi a 2019 da 2023, ba zata yi aiki yanzu ba domin mutane sun fahimce su.

“Masu zaɓe a Kano yanzu sun san waɗanda ke amfani da su wajen kasuwancin siyasa, har ma da fitattun ‘yan siyasa sun gane dabarun ‘yan kasuwar siyasa,” inji Nabena.

Jigon APC ya ƙalubalanci Kwankwaso kan tituna

Kara karanta wannan

Sukar gwamnati: Jam'iyyar NNPP ta ba Tinubu shawara kan Kwankwaso

Dangane da lalacewar hanyoyi, Nabena ya ƙalubalanci jagoran NNPP da ya yi tafiya ta hanyar mota a jihohin Kudu maso Kudu, domin ya kwatanta hanyoyin da ke yankin da na Arewa.

Ya ƙara da cewa:

“Shin Arewa ce a ƙasan Kudu ne ko kuwa Kudu ta fi Arewa? Bayan shekara takwas Arewa na mulki, me yasa har yanzu Kwankwaso ke kuka da rashin ci gaba a Arewa?
"Kuma da wane kuɗin Arewa aka gina Kudu, zinari ne, shinkafa ko kuma gyada?”
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Jigon APC ya ce yan Arewa ba za su yarda da kalaman Kwankwaso ba Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Abin da ya sa Kwankwaso ya soki Tinubu

A cewar Nabena, Kwankwaso yana ƙoƙarin harzuƙa ƴan Arewa da Kudu don hana Kudu kammala wa’adinta na shekaru takwas a fadar Shugaban Ƙasa, amma ba zai yi nasara ba.

Ya ƙara da cewa masu kaɗa kuri'a a Arewa ba za su yarda da irin waɗannan hujjoji marasa tushe ba, cewar rahoton The Nation.

“Ba za ka iya tsoratar da Kudu ko wani yanki da kuri’un Kano ba. Mun gane wasan, kuma mun san abin da kuke nema. Zamanin amfani da addini ko kabila ya wuce,” inji shi.

Kara karanta wannan

"Ku ankara": NNPP ta yi kira da babbar murya ga matasan Arewa kan Kwankwaso

Hadimin Tinubu ya musanta zargin Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa hadimin shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya musanta zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Tinubu na nunawa Arewa wariya.

Abdul'aziz ya ce gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da ayyukan tituna a faɗin ƙasar nan ba tare da nuna wariya ga kowane yanki ba.

Ya ce idan jama'a suka duba za su ga dukkan ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi na matakin ƙasa ne, babu zancen Kudu ko Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel