Gwamnoni 2 da Ƴan Majalisar Tarayya Za Su Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar Haɗaka ADC

Gwamnoni 2 da Ƴan Majalisar Tarayya Za Su Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar Haɗaka ADC

  • Jam'iyyar ADC reshen Kudu Maso Gabashin Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta karɓi gwamnoni biyu da ƴan Majalisar Tarayya
  • Mataimakin shugaban ADC na ƙasa mai kula da Kudu maso Kudu, Chilos Godsent ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
  • A cewarsa, wannan wani ɓangare ne a ƙoƙarin da suke na samun goyon bayan al'ummar yankin a babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jam'iyyar haɗakar ƴan adawa watau ADC ta bayyana cewa tana shirye-shiryen karɓar gwamnoni biyu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kwamitin zartarwa na ADC (ZWC) reshen Kudu maso Gabas ne ya bayyana hakan, ya ce gwamnonin sun amince za su baro jam'iyyunsu, su dawo ADC.

Jam'iyyar ADC za ta fara karɓar gwamnoni.
ADC ta ce gwamnoni 2 a yankin Kudu maso Gabas sun amince za su shiga haɗaka Hoto: @ADCCoalation
Source: Twitter

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mataimakin shugaban ADC na Kudu maso Gabas ya rabawa manema labarai.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan APC ya fadi shirin da suke yi kan hadakar 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 2 za su shiga haɗakar ADC

Ya tabbatar da cewa tuni tattaunawa da neman shawarwari suka yi nisa kuma nan ba da jimawa ba waɗannan gwamnoni za su fito su sanar da jama'a shirinsu.

A cewarsa, idan aka kammala komai gwamnonin guda biyu za su sanar da sauya sheƙa a hukumance zuwa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya, rahoton Punch.

Legit Hausa ta tattaro cewa tun bayan kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗakar ƴan adawa, manyan ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban suka fara tururuwa zuwa cikinta.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi na daga cikin fitattun ƴan adawa da ke jagorantar wannan tafiya.

Jam'iyyar ADC ta lashi takobin cewa za ta ƙwato mulkin Najeriya daga hannu shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ta ce ya kawo yunwa da matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa gwamnonin PDP da APC ba su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC ba'

Mataimakin shugaban ADC na ƙasa (Kudu Maso Gabas), Chilos Godsent, ya ce gwamnonin yankin biyu sun aminta za su shigo wannan tafiya ta ceto Najeriya.

Ƴan Majalisar Tarayya da na jihohi za su shiga ADC

Ya bayyana cewa hakan wani ɓangare ne na ƙudurin yankin na tabbatar da cewa Kudu Maso Gabas ya ba jam’iyyar ADC gudummawar da ake buƙata a babban zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa wasu ‘yan majalisar wakilai ta ƙasa da na majalisar dokoki ta jihohi suma za su sanar da niyyarsu ta shiga jam’iyyar (ADC) cikin watanni masu zuwa.

Taron hadakar yan adawa ta ADC.
ADC ta yi ikirarin cewa ta fara karbuwa a wurin gwamnoni da ƴan Majalisa Hoto: @Atiku
Source: Twitter

A cewarsa, wani ɗan majalisar wakilai da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya faɗa masu cewa:

“Mun yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC ne domin haɗa ƙarfi da sauran ‘yan haɗaka wajen kifar da gwamnatin Ahmed Bola Tinubu wacce ta jefa ƙasa cikin talauci da wahala a 2027.”

Atiku ya hasaso nasarar ADC a zaɓen 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran ƴan adawa a Najeriya. Atiku Abubakar, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ADC za ta shiga fadar shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce yana da yaƙinin cewa shirin da suka yi, zai ba su gagarumar nasara idan aka fita kaɗa kuri'a a zaɓe mai zuwa.

Ya ce ADC ta zo da wani tsari da manufofi don magance matsalolin tattalin arziki da sauran kalubalen ƙasa da suka dabaibaye al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262