Majalisar Tarayya za Ta Yi Sauyi kan Zaben Shugaban Kasa da Gwamnoni a 2027

Majalisar Tarayya za Ta Yi Sauyi kan Zaben Shugaban Kasa da Gwamnoni a 2027

  • Majalisar Wakilai ta gabatar da kudirin sauya dokar zaɓe domin gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda daga shekarar 2027
  • Haka zalika za a rage kashe kuɗi wajen zaɓe, inda shugaban ƙasa zai kashe N10bn, gwamnoni N3bn, sai ‘yan majalisa N250m
  • Jam’iyya za ta iya sauya ɗan takara ne kawai idan ya mutu ko ya janye, kuma sai an sake yin zaɓen fitar da gwani cikin kwanaki 14

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta gabatar da wani sabon kudiri da ke nufin yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta 2022.

Babban abin da kudirin ya ƙunsa shi ne gudanar da dukkan zaɓukan shugaban ƙasa, ‘yan majalisar dattawa, ‘yan majalisar wakilai, gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a rana guda.

Kara karanta wannan

An daure wanda ya kagi labarin rasuwar Bola Tinubu a mummunan yanayi

'Yan majalisar wakilai suna muhawara a zauren majalisa
'Yan majalisar wakilai suna muhawara a zauren majalisa. Hoto: House of Representative, Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Jaridar the Nation ta wallafa cewa baya ga sauyi a ranar zabe, ana neman kawo sauyi a wasu abubuwan da suka shafi kada kuri'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Ana so a dawo da zabuka a rana 1

Kudirin da Shugaban Kwamitin Majalisa kan Harkokin Zaɓe, Bayo Balogun ya gabatar ya bukaci sauya tsarin zabe a Najeriya.

An ji cewa kudirin na neman a bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) hurumin shirya dukkan zaɓuka na ƙasa da jihohi a rana ɗaya.

Wasu sharuddan zabe da ake so a kawo

Kudirin dokar ya tanadi biyan kuɗin rajista har Naira miliyan 50 ga kowace ƙungiyar siyasa da ke neman rijista da INEC a matsayin jam'iyya.

Rahoton ABC News ya nuna cewa ana nufin takaita yawan kuɗin da ‘yan takara za su kashe zuwa:

  • Zaɓen shugaban ƙasa – N10bn
  • Zaɓen gwamna – N3bn
  • Sanata – N500m
  • Dan majalisar wakilai – N250m
  • Dan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi – N30m
  • Kansila – N10m

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Dokar na da nufin hana wata kungiya ko mutum ɗaya bayar da gudunmawar da ta wuce Naira miliyan 500 ga ɗan takara.

Shugaban hukumar zabe ta kasa, Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Mahmood Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Source: UGC

Sauyi a zaben maye gurbi a Najeriya

Domin rage yawan zaɓukan cike gurbi da ake yi bayan mutuwa ko murabus ɗin ‘yan majalisa, kudirin ya ba jam’iyya hurumin maye gurbi ba tare da sake gudanar da zaɓe ba.

Dokar ta kuma tanadi cewa idan aka samu wani gurbi cikin kwanaki 90 kafin zaɓe, dole a cike shi cikin kwanaki 30.

Sabuwar dokar zabe kan 'yan takara

A karkashin kudirin, kowane ɗan takara zai gabatar da takardun shaidar cancanta tare da rantsuwa a kotun tarayya ko ta jiha.

Hukumar INEC za ta wallafa sunan da bayanan ɗan takarar a yankin da zai tsaya zaɓe cikin kwanaki 21.

Duk wani mai neman takara daga cikin jam’iyya na iya kai ƙara kotu idan yana da hujjar cewa akwai matsala a tattare da bayanan abokin takarar shi.

Baya ga haka, idan kotu ta tabbatar da hakan, za a soke takarar kuma jam’iyyar za ta fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

'Kungiyoyi na tururuwa zuwa INEC, masu neman zama jam'iyyu sun kai 144

Kungiyoyi na neman rajista da INEC

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa ta samu karin masu bukata a musu rajistar jam'iyya.

Hakan na zuwa ne bayan 'yan adawa a Najeriya da sauran masu fafutuka sun mika bukatar INEC ta musu rajistar sababbin jam'iyyu.

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa sannu a hankali za ta rika fitar da bayanai kan halin da ake ciki game da bukatun rajista na kungiyoyin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng