2027: Gwamnan APC Ya Fadi Shirin da Suke Yi kan Hadakar 'Yan Adawa

2027: Gwamnan APC Ya Fadi Shirin da Suke Yi kan Hadakar 'Yan Adawa

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa APC ba za ta tsaya ta zura ido tana kallon 'yan hadakar adawa ba
  • Ya bayyana cewa yayin da suke irin na su shirin, su ma a APC suna ci gaba da tsara dabarun neman samun nasara
  • Gwamnan ya kuma yi albishir da cewa nan ba da jimawa ba, wani gwamna zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi nuni da yiwuwar shigar wasu fitattun ‘yan siyasa cikin jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.

Gwamna Sule ya yi watsi da zarge-zargen barazana da yi wa 'yan adawa bita da kulli da ake dangantawa da jam’iyyar mai mulki.

Gwamna Sule ya tabo batun hadaka
Gwamna Sule ya ce APC na shiri kan 'yan hadaka Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya lashe amansa, ya faɗi dalilin janye neman takarar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadaka ta sa jam'iyyar APC ta fara shiri

Gwamna Sule ya bayyana cewa APC na ci gaba da tsara dabaru gabanin babban zaɓen shekarar 2027, musamman bayan bayyanar hadakar jam’iyyun adawa.

Lokacin da aka tambaye shi ko gwamnonin APC sun tattauna illar da wannan sabuwar hadakar zata iya haifarwa, ya amsa da ce cewa eh sun tattauna.

"Eh, mun tattauna. Amma ba wani abu bane da zan bayyana a nan. Kamar yadda su ke shirinsu, mu ma muna da namu shirye-shiryen. Siyasa ce mu ke yi."
"Ba za mu zauna mu zura ido suna ta shiri ba. Kamar yadda su ke tsara dabaru, mu ma muna yi. A ƙarshe dai, wanda ya fi tsara dabaru zai yi nasara."
"Muna kara samun karin gwamnonin PDP da ke sauya sheƙa zuwa APC. Ba da daɗewa ba, za ku ji wani sabon gwamna ya koma APC."
"Kullum kuna jin labarin sanata ko ɗan majalisa yana ficewa daga jam’iyyar adawa zuwa APC. Wannan ba sihiri ba ne, shiri ne mai zurfi da tsari."

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa gwamnonin PDP da APC ba su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC ba'

- Gwamna Abdullahi Sule

Jam'iyyar APC ba ta raina adawa

Lokacin da aka tambaye shi kan zargin da jam’iyyar ADC ta yi cewa wasu ‘yan siyasa na jin tsoron shiga hadakar adawa saboda tsangwama daga gwamnatin APC, Gwamna Sule ya ƙaryata hakan.

Abdullahi Sule ya magantu kan hadaka
Gwamna Sule ya ce APC na shiri kan hadaka Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook
"Ni ba na raina kowa, amma su dai dole su faɗi wani abu. Lokacin mulkin Jonathan ba irin abubuwan da muke gani yanzu ake gani ba. Ba mu fuskanci irin kalubalen da muke ciki a yanzu lokacin Jonathan ba."
"Mutanen da suka haɗu suka kafa APC irin su ANPP, APGA, ACN, CPC da kuma sabuwar PDP, ba su da kama da irin waɗanda suka haɗu a wannan sabuwar hadakar 'yan adawa."

- Gwamna Abdullahi Sule

ADC ta fadi 'dan takarar da take goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi magana kan dan takarar da take goyon baya don kifar da Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnonin da suka hana Peter Obi, Wike ziyartar jihohinsu a 2025

ADC ta bayyana cewa ba ta da wani dan takara daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa da take goyon baya.

Ta bayyana cewa ta dukufa wajen samar da sabon tsarin siyasa gabanin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng