ADC: Sanata a PDP Ya Ayyana Atiku a Matsayin Jagoran Siyasar Arewa
- Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Dankwambo, ya bayyana Atiku a matsayin jagoran Arewa duk da ya bar PDP
- Dankwambo ya ce a yanzu sun fi mayar da hankali kan gina jam’iyyar PDP, ba batun wanda zai tsaya takara a 2027 ba
- Sanatan na PDP ya kara da cewa Kashim Shettima da Namadi Sambo ma shugabanni ne da suka cancanci girmamawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar Gombe ta Arewa, Sanata Ibrahim Dankwambo ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne jagoran siyasar Arewa.
Dankwambo ya fadi haka ne yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Gombe, inda ya jaddada cewa ba matsayin jam’iyya ke ba da jagoranci ba.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya ce duk da Atiku ya bar jam'iyyar PDP, hakan ba zai hana shi zama jagora ba.
Sanata Dankwambo ya ce:
"A halin yanzu lokaci ne na gina jam’iyyarmu. Ko da Atiku Abubakar yana PDP ko ADC, a gare mu dan Arewa ne, kuma shi ne jagoranmu. Mun yarda da shi, kuma muna sonsa."
Dankwambo ya yabi wasu manyan Arewa
Dankwambo ya ambaci sauran manyan ‘yan siyasa daga Arewa da ya ce su ma suna da matsayi, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Namadi Sambo.
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Kashim Shettima shugaba ne. Shi ne mataimakin shugaban kasa, kuma dan wannan yanki ne. Muna sonsa kuma muna fatan ya shigo jam’iyyarmu. Namadi Sambo ma hakanan.”
Sanatan ya kuma bayyana cewa baya da wata niyya ta sake takarar shugaban kasa a 2027, yana mai cewa gina jam’iyya yafi dacewa a halin yanzu.
PDP ta kammala zaben cikin gida
Dangane da ci gaban jam’iyyar PDP a matakin kasa, Dankwambo ya bayyana cewa jam’iyyar ta kammala zabubbukan cikin gida daga matakin mazabu har zuwa na shiyya.
Ya ce:
"A taron da aka yi kafin taron NEC, muna bukatar fadakar da mambobinmu kan al’amuran da suka shafi jam’iyya a matakin kasa.
"A yau, PDP ce kadai jam’iyya da ta kammala zabubbuka daga matakin mazabu, kananan hukumomi, jiha da shiyya."
Ya kuma ce an riga an tsara ranar babban taron kasa na jam’iyyar wanda zai amince da sauran batutuwan cikin gida.

Source: Facebook
Maganar Sanata Siyako kan rikicin PDP
Sanata Anthony Siyako da ke wakiltar Gombe ta Kudu a majalisar dattawa, ya karyata jita-jitar da ke cewa PDP na cikin rikici a jihar bayan ficewar wasu da matsalolin cikin gida.
A cewarsa:
“Muna so mu cire shakku daga zukatan jama’a. Ganin cewa duka mambobin majalisar tarayya da na jiha suna nan, hakan na nuna cewa komai lafiya lau.”
Edo: Atiku Abubakar ya kare Peter Obi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan maganar gwamnan jihar Edo.
Bayan wata ziyara da Peter Obi ya kai Edo, gwamnan jihar ya gargade shi da kar ya kawo irin ziyarar har sai ya sanar da shi.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa hakan bai dace ba kuma yana goyon Peter Obi na cewa yana da 'yancin shiga jihar a ko da yaushe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


