Gwamna Dankwambo ya rushe majalisarsa
A ranar Talata ne gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya rushe majalisar zartarwa ta jiha tare da sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na karshe da ya yi da masu rike da mukaman siyasa a ranar Talata.
Dankwabo ya shaida wa masu rike da mukaman siyasar da ya sauke cewar yana yi musu fatan alheri a ayyuka da harkokin da za su shiga a nan gaba tare da yi musu godiya bisa gudunmawar da suka bashi da jihar Gombe.
A cewarsa, akwai bukatar yiwa dukkan al'ummar jihar godiya saboda suma sun bayar da hadin kai wurin nasarar da gwamnatinsa ta samu.
DUBA WANNAN: Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame
Ya kuma mika godiyarsa ga jam'iyyar PDP saboda bashi damar yin takarar zabe a karkashinta inda ya yiwa jiharsa hidima na tsawon shekaru takwas.
Gwamnan mai barin gado ya kuma tuna diyarsa da ta rasu a shekarar 2014 inda ya ce rasuwar ta babban rashi ne gareshi duba da cewar ta rasu tana da kananan shekaru.
"Tana tare da ni lokacin da aka rantsar da ni mulki a 2011 amma a halin yanzu ba ta nan lokacin da zan mika mulki ga sabuwar gwamnati. Ba mu manta da tsohon Attorney Janar kuma kwamishinan shari'ar na jihar mu, marigayi Barrister Abdulhameed Ibrahim da ya rasu a bakin aiki.
"Muna kuma mika godiyar mu ga sarakunan gargajiya musamman Sarkin Gombe, Shehu Usman Abubakar da dukkan wadanda suka taimaka wurin nasarar da muka samu amma ba su samu tsawon ran ganin wannan ranar ba," inji shi.
Dankwambo ya taya zababen gwamna, Muhammad Inuwa Yahaya murnar lashe zabe kuma ya bukaci al'ummar jihar su bashi hadin kai domin ciyar da jihar gaba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana
Asali: Legit.ng