An Gano Miliyoyin da aka Tara domin Tallata Tinubu a Zaben 2027
- Rahotanni na nuni da cewa kungiyar SERHA daga Kudu maso Gabas ta tara Naira miliyan 200 don tallafa wa Bola Tinubu a 2027
- Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin kaddamar da reshen ta a jihar Imo tare da raba kayan tallafi ga al'umma da suke bukata
- SERHA ta ce sababbin ayyukan layin dogo da hukumar raya Kudu maso Gabas da aka kafa suna tabbatar da adalci da aka yi musu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata babbar kungiya mai mara wa Bola Ahmed Tinubu baya daga yankin Kudu maso Gabas ta sanar da cewa fara tara masa gudumuwa.
Kungiyar ta tara Naira miliyan 200 don sayen fom din neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da kuma daukar nauyin yakin neman zabe a 2027.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa kungiyar SERHA ta bayyana hakan ne a yayin wani taron kaddamar da reshenta a Imo da kuma raba kayan tallafi ga al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki na SERHA ya nuna goyon bayan siyasa mai karfi daga yankin Kudu maso Gabas ga shugaban kasa Tinubu, tare da bukatar ci gaba da aiwatar da manufofinsa.
SERHA ta tarawa Bola Tinubu miliyoyi
Shugaban kungiyar ta SERHA na kasa, Hon. Belusochukwu Enwere, ya bayyana a jawabinsa cewa sun kuduri aniyar ganin Shugaba Tinubu ya zarce a zaben 2027.
Ya ce:
“A yau, muna mika takardar cike alƙawari na Naira miliyan 200 don sayen fom din neman takara da sauran shirye-shiryen yakin neman zabe.
"Muna nan a shirye don yada ayyukan Tinubu a dukkan kananan hukumomi da gundumomi.”
Ya yabawa shugabancin Tinubu bisa gyaran abubuwan more rayuwa, ci gaban ilimi da bai wa kowane yanki damar shiga harkokin gwamnati, musamman Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa
Meyasa SERHA ke son Tinubu?
Enwere ya ce ayyuka kamar layin dogo na yankin da gwamnatin tarayya ta amince da shi na Dala biliyan 3, wani babban ci gaba ne da zai taimaka wajen kasuwanci da rage kudin sufuri.
The Guardian ta rahoto ya ce:
“Wannan aikin layin dogo zai sauya al'amura a yankinmu, kuma ya kawar da koke-koken cewa ana nuna mana wariya.”
Ya kara da cewa kafa hukumar SEDC wata alama ce da ke nuna yadda gwamnatin tarayya ke da niyyar bunkasa yankin.

Source: Facebook
Shugaban SERHA ya ce daga watan Agusta, za su fara zagaye dukkan kananan hukumomi 95 da gundumomi 2,344 na yankin domin karfafa goyon bayan Tinubu a matakin tushe.
Bayan haka, an raba kayan tallafi kamar babura, motoci ƙanana, keken dinki, kayan gyaran gashi da tallafin kuɗi domin ƙarfafa sana’o’in matasa da cigaban al’umma.
An kama wanda ya ce Tinubu ya mutu
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar DSS ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da yada labarin cewa Bola Tinubu ya rasu.
Matashin da aka kama dan asalin jihar Kano ne kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotu domin gabatar masa da tuhume tuhume.
Sai dai wasu bayanai da aka samu daga wani lauya sun nuna cewa ba matashin ba ne ya hada bidiyon da ake zargin shi a kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

