'An Buga An Bar Mu,' Kwankwaso Ya Faɗi Abin da Ya Sa Kwankwasiyya Ta Gagara

'An Buga An Bar Mu,' Kwankwaso Ya Faɗi Abin da Ya Sa Kwankwasiyya Ta Gagara

  • Jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ba za a iya kayar da Kwankwasiyya a Kano ba
  • Ya ƙara da cewa akidar tafiyar ta kafu ne kan gina ɗan adam da ilimi, kuma ta yi matukar karɓuwa a tsakanin al’umma
  • Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnoni da su zuba jari a ilimi da ci gaban bil’adama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alfahari da mabiyansa.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙara da bayyana cewa babu wani da zai iya kara wa ko ya kawo matsala ga tafiyar siyasar Kwankwasiyya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Ku ankara": NNPP ta yi kira da babbar murya ga matasan Arewa kan Kwankwaso

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya ya yi alfahari da mabiyansa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

PM News ta wallafa cewa Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan jami'ar Northwest ta karrama shi da digirin girmamawa a fannin ilimi.

Kano: Kwankwaso ya yi alfahari da Kwankwasiyya

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa duk wani ɗan siyasa da ke tafiya da akidar Kwankwasiyya zai samu goyon bayan jama'a.

Ya ce kwazon Kwankwasiyya wajen zuba jari don gina ɗan adam ya sa ta zama hanya mafi tasiri da ɗan siyasa zai iya bi don cimma manufarsa a Kano da Arewacin Najeriya.

Ya ce:

"Ba za ka iya kayar da tafiyar siyasar Kwankwasiyya ba. Muna ko'ina, kuma hakan ya samo asali ne daga kyakkyawan aikin da muka yi. Wannan shi ne samar da ci gaban dan Adam."

Kwankwaso ya ƙara da cewa samar da ilimi mai sauƙi a tsakanin talakawa zai taimaka wajen cicciɓa al'umma da gina ɗan adam.

Kara karanta wannan

Minista ya soki Kwankwaso da ya taba Tinubu, ya masa gorin ƙuri'un Buhari miliyan 12

Shawarar Sanata Kwankwaso ga ƴan siyasa

Tsohon ministan tsaron ya ce a lokacin da yake gwamnan Kano, ya zuba jari mai yawa a harkar ilimi.

Ya ce wannan ya sa dubunnan matasa daga jihar suka samu guraben karatu a makarantun gaba da sakandare a kasashen waje.

Kwankwaso ya nuna farin cikinsa da yadda yawancin waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatun nasa yanzu haka malamai ne a manyan jami’o’i a Kano da sauran sassan kasar.

Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
Kwankwaso ya ce babu mai iya kayar da Kwankwasiyya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Kwankwaso ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran gwamnoni a fadin kasar da su zuba jari sosai a ilimi da tabbatar ci gaban dan Adam.

Ya nanata cewa akidar Kwankwasiyya na da kishin ganin kowane yaro a Najeriya na samun ilimi kyauta ba tare da tangarɗa ba.

Masoyin Kwankwaso: 'Za mu zaɓi jagora'

Muhammad Lawan, ɗaya daga cikin mabiya tafiyar siyasar Rabi'u Musa Kwankwaso ne a Kano, ya shaida wa Legit cewa suna fatan jagoransu ya yi shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Dalilin jam'iyyar APC na neman Rabi'u Musa Kwankwaso

A kalamansa:

Mun yarda da Kwankwaso 100% kuma ko yanzu ya tsaya takarar shugaban kasa za mu zaɓe shi."
"Idan ya sauya sheƙa, za mu bi shi, idan ya zauna a NNPP za mu zauna, amma matasanmu da tsofaffi duka ƴan Kwankwasiyya ne."

Muhammad Lawan ya kara da cewa Kwankwaso yana taimakon matasa, kuma abokansa da yawa sun samu tagomashin zuwa ƙaro karatu a ƙasashen waje.

Ministan Tinubu ya dura kan Kwankwaso

A baya, kun ji cewa Ministan Ayyuka na ƙasa, Injiniya David Umahi, ya mayar da martani mai zafi kan sukar da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa Bola Tinubu.

Umahi ya zargi Kwankwaso da yada ƙarya domin yaudarar al’ummar Arewa da kuma neman gina kansa a matsayin jigo a siyasar yankin. Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita Kudu wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa, da watsi da yankin Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng