Zaɓen 2027: Dalilin Jam'iyyar APC na Neman Rabi'u Musa Kwankwaso
Hankulan manyan jam’iyyun ƙasar nan da sauran masu ruwa da tsaki a fagen siyasa sun karkata zuwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, musamman a makon da ya gabata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tun bayan halartar da Sanata Kwankwaso ya yi wani taro da aka gudanar a fadar shugaban kasa, jita-jita ke cewa jagoran jam’iyyar NNPP zai iya koma wa APC.

Asali: Facebook
BBC ta wallafa cewa wasu muhimman abubuwan da suka faru a jam’iyyar APC mai mulki a ’yan kwanakin baya sun kara rura wutar rade-radin sauya shekar Kwankwaso.
Legit ta kuma tattauna da masanin siyasa daga jihar Kano, Farfesa Habu Muhammad Fagge, wanda ya bayyana wasu muhimman dalilin da APC ke kokarin jawo Kwankwaso zuwa cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan jam'iyyar APC na neman Kwankwaso
Farfesa Habu Muhammad Fagge, gogaggen mai sharhi kan lamurran siyasa a jihar Kano, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso na da karfin mabiya a fadin kasar nan, musamman a Arewa.
Ya shaidawa majiyar Legit cewa wannan shi ne karo na uku ko na hudu da jam’iyyar APC ke kokarin jawo Kwankwaso ya sauya sheka zuwa cikinta.
Ya ce:
“Alamu na nuna cewa akwai ’yar fahimtar juna tsakaninsu, ko da kuwa ta fuskar shawarwari ce. Amma idan aka dubi baya, watakila abin da ya hana mu’amalarsu yin armashi shi ne kasancewar Abdullahi Umar Ganduje a cikin jam’iyyar APC da kuma zamansa shugaban jam’iyyar a matakin kasa."
Farfesa Fagge ya kara da cewa:
“Yanzu da babu Ganduje, da alama ba zai sake samun wata matsayi mai tsoka a siyasa ba. Don haka, ina ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai iya kokarin jawo Kwankwaso zuwa APC.”
Tasirin Kwankwaso ga siyasar 2027
Farfesa Habu Fagge ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso ya sauya sheƙa idan magana ta faɗa da APC.

Asali: Facebook
Farfesa Habu Fagge ya ƙara da cewa:
"Kwankwaso ya zama mutum 1 tamkar da 10 domin an fahimci cewa yana da mutane."
"Yanzu babbar matsalar a nan shi ne 'yan hamayya sun tattara a ADC, kuma shi Kwankwaso bai nuna sha'awa shiga cikinsu ba."
Ya ƙara da cewa rashin nuna sha'awar haɗin kai da ƴan adawa na nuna cewa akwai wata a ƙasa.
Farfesa Fagge ya ce idan ciniki ya faɗa da APC, hakan zai shafi siyasar 2027 fiye da yadda ake tsammani.
Yadda Kwankwaso ya kankaro darajarsa
A nasa bangaren, Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS) da ke Kano, ya ce Kwankwaso ya kara samun daraja bayan zaben shugaban kasa na 2023.
A cewarsa, kuri’un da Kwankwaso ya samu a jihar Kano shi kadai a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP ya daga darajarsa.
Ya ce:
“Idan aka duba kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da ya gabata, da kuma irin tazarar da ke tsakaninsa da jam’iyyar APC, da yadda jam’iyyarsa ta NNPP ta samu nasarori a matakin jiha."
"Hakan na iya sanya APC tunanin cewa zai fi amfani a jawo Kwankwaso domin su kwashe wadancan kuri’un gaba daya maimakon samun kaso 25 kacal."
Sufi ya kara da cewa:
“Haka su ma sauran jam’iyyun, musamman jam’iyyun hadaka da ke kira ga Kwankwaso da ’yan hamayya irinsa, babban abin da suke kwaɗayi shi ne yawan kuri’un da Kwankwaso ke da su a Kano da ma sauran sassan Arewa.”
Kwankwaso ya yi magana kan ƙarfin Kwankwasiyya
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta zama ginshikin da ba za a iya karya ba a siyasar jihar Kano.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan da jami’ar Northwest da ke Kano ta karrama shi da digirin girmamawa a fannin ilimi.
Tsohon gwamnan Kano ya ƙara da bayyana cewa kowane ɗan siyasa da ya rungumi akidar Kwankwasiyya tabbas zai samu abin da ya ke nema a siyasarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng