Tinubu: An Yi Hasashen Wanda Zai Zo na 1, na 2, na 3 da na 4 a Zaɓen Shugaban Ƙasar 2027

Tinubu: An Yi Hasashen Wanda Zai Zo na 1, na 2, na 3 da na 4 a Zaɓen Shugaban Ƙasar 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam'iyyar PDP ya ce Shugaba Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027
  • Ayo Fayose ya ce Bola Tinubu mutum ne mai wayau da dabara, kuma alamu sun nuna ya gama kama ƙuri'un Kudu, kaɗan yake buƙata a Arewa
  • Fayose ya kuma yi hasashen cewa Peter Obi zai sake ba da mamaki, yana mai cewa shi zai zo na biyu a sakamakon ƙuri'un da za a kaɗa a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi hasashen cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben 2027.

Fayose ya yi ikirarin cewa shugaban kasa ya gama kama Kudancin Najeriya, ƙuri'u kaɗan yake buƙata daga ƴan Arewa domin nasararsa ta tabbata.

Kara karanta wannan

'Yadda matata ta hana ni sukar Buhari bayan ya mutu': Tsohon gwamna ya magantu

Fayose da Shugaba Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya ce Bola Tinubu ne zai ci zaɓen 2027 Hoto: @AyoFayose, @OfficialABAT
Source: Twitter

Ayo Fayose ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya yi hasashen cewa jam’iyyar PDP za ta kare a matsayi na hudu, jam'iyyar haɗaka watau ADC za ta zo na uku, yayin da Peter Obi zai zo na biyu a sakamakon zaɓen 2027.

Yadda Bola Tinubu zai ci zaɓen 2027

A rahoton Daily Trust, Fayose ya ce:

“Tinubu, tun kafin ya hau mulki ya haɗa APC, ya ɗaga darajarta, ya kayar da PDP a 2015. A 2023 ma, ba tare da haɗin gwiwar ‘yan adawa ba, ya tumurmusa kowa a zaɓe.
"Kuna tunanin mutumin da bai fiye magana ba, ba shi da wayo? Da ni ma ina da damar da yake da ita, da tuni na wuce haka. Mutumin nan ya gama kama Kudu, kaɗan yake buƙata a Arewa ya ci zaɓe.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Atiku, an yi hasashen matsayi da PDP za ta ƙare a sakamakon zaɓen 2027

“Peter Obi zai ba da mamaki kowa ya san haka. Obi zai fi PDP samun ƙuri’u. PDP za ta zo ta hudu, ADC ta uku, APC ta farko, Obi zai zo na biyu, ka rubuta ka ajiye."
Atiku, Bola Tinubu da Peter Obi.
Fayose ya bayyana cewa Obi zai sake ba da mamaki a zaɓen 2027 Hoto: @Atiku, @OfficialABAT, @PeterObi
Source: Facebook

Ƴan Najeriya na kama maganar Fayose?

Dangane da batun ko ƴan Najeriya na kama maganarsa, tsohon gwamnan ya ce bai damu ba, wanda ya ga dama ya yarda, wanda bai ga dama ba kar ya yarda.

"Ba dole ne mutane su yarda da ni ba. Wannan ba damuwata ba ce. Ka san halin da jam’iyyarmu ke ciki a yau. Kuma addu’ata ita ce PDP ta zo ta hudu a zaɓe mai zuwa.”

PDP ta sauya wurin gudanar da taronta na ƙasa

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta sauya wuri da lokacin gudanar da babban taronta na ƙasa wanda za a zaɓi sababbin shugabanni.

PDP ta sanya ranar Asabar, 15 ga Nuwamba 2025 zuwa Lahadi, 16 ga Nuwamba, 2025 a matsayin ranakun da za ta gudanar da zaɓen shugabannin jam'iyya na ƙasa.

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya sanar da cewa jam'iyyar ta sauya wurin gudanar da taron zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262