Ana Maganar Haɗaka, Zaman El Rufai na Tangal Tangal a SDP bayan Matsayar Jam'iyyar

Ana Maganar Haɗaka, Zaman El Rufai na Tangal Tangal a SDP bayan Matsayar Jam'iyyar

  • Jam’iyyar SDP ta yi zazzaffan kalamai game da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
  • SDP ta nesanta kanta da Nasir El-Rufai, tana cewa ba mambanta ba ne, kuma baya da izini ya wakilci jam’iyyar ko magana da sunanta
  • Ta bayyana cewa ba a taba ba El-Rufai wani matsayi a jam’iyyar ba, kuma ba ya cikin rajistar mambobin SDP

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta SDP a Najeriya ta fadi matsayarta game da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Jam'iyyar ta nesanta kanta da tsohon gwamnan inda ta ce ba dan SDP ba ne kuma bai da wani iko a cikinta.

SDP ta barranta kanta da El-Rufai
Jam'iyyar SDP ta ce El-Rufai ba mambanta ba ne. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Matsayar SDP game da tsohon gwamna El-Rufai

Sakataren yankin Arewa maso Yamma na jam'iyyar, Idris Inuwa shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris Inuwa ya ce Nasir El-Rufai ba mamban jam'iyyar ba ne kuma ba zai iya wakiltar SDP ba.

Har ila yau, Inuwa ya ce El-Rufai bai cikin rajistar mambobin jam’iyyar da aka adana saboda hujjoji.

Ya ce

“Mun samu labarin cewa Malam Nasir El-Rufai yana shiga taruka da tattaunawa yana ikirarin cewa yana magana da sunan SDP.
“Bari a bayyana: El-Rufai ba shi da izini, ba a yarda da shi ba kuma ba a amince da wakilcinsa daga SDP ba.
“Dukkan abubuwan da ya aikata ya yi su ne ba tare da sanin ko amincewar shugabancin jam’iyyar ba, ciki har da mukaddashin shugabanta, Sadiq Umar.”
SDP ta nesanta kanta da Nasir El-Rufai
Jam'iyyar SDP ta tabbatar da cewa El-Rufai ba mambanta ba ne. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Facebook

El-Rufai: An bayyana jagororin SDP a Najeriya

Inuwa ya sake tabbatar da shugabancin Umar, sakataren jam'iyar, Olu Agunloye, da dan takarar shugaban kasa a 2023, Adewole Adebayo, a matsayin jagororin SDP.

Sakataren jam'iyyar SDP ya bukaci a yi watsi da duk wani jawabi da El-Rufai ya fitar da sunan jam’iyyar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fito fili ya fadi wadanda suka assasa matsalolin jam'iyyar

Ya kuma zargi Umar Ardo da kirkirar wata sabuwar kungiya ta siyasa yana fakewa da jam’iyyar SDP mai adawa a kasar.

“Mun kada kuri’ar rashin amincewa da El-Rufai. Muna kira da a dakatar da Dr Umar Ardo daga SDP nan take.
“Kokarinsa na amfani da jam’iyya hanya ce ta nuna gazawa da rashin dabarar siyasa.
“Wannan gargadi ne na karshe: ku daina damfarar siyasa, ko kuma NEC zai kafa kwamiti don bincike da fallasa su.”

- Cewar sanarwar

Ana fargabar El-Rufai zai iya barin haɗaka

Kun ji cewa rikicin cikin gida da ke ci gaba da kunno kai a jam’iyyar ADC na barazana ga karfi da hadin kan 'ya'yanta tun kafin zaben 2027.

Wasu majiyoyi sun ce burin Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 a ƙarƙashin ADC ya jawo sabani tsakanin wasu da ke cikin tafiyar.

Wasu na ganin Atiku zai shiga ADC don cimma muradinsa kawai, yayin da Nasir El-Rufai ya dage cewa a ba dan Kudu tikiti a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.