Ana sa Ran zai Bar NNPP, Kwankwaso ya Bada Kafa da Ya karbi 'Yan APC a Kano

Ana sa Ran zai Bar NNPP, Kwankwaso ya Bada Kafa da Ya karbi 'Yan APC a Kano

  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ba jama'a mamaki a daidai lokacin da ake ikirarin zai sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki
  • A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025, Sanata Kwankwaso ya karbi dubunnan magoya bayan APC zuwa jam'iyya mai-ci a Kano
  • Ya shaida wa jama'a cewa NNPP tana da shugabanci na gari, wanda haka ne daya daga cikin dalilan da jama'a ke tururuwa zuwa cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC, sai ga shi ya ba da mamaki a jihar Kano.

A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025, Sanata Kwankwaso ya karɓi magoya bayan APC kwana guda da jam’iyyar ta bayyana cewa a shirye take ta karɓe shi idan zai dawo.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Kwankwaso ya karbi yan APC
Kwankwaso ya ce akwai jagoranci nagari Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce tsarin shugabanci a jihar Kano da irin sahihin jagorancin siyasa da suke da shi ne ke janyo mutane su shiga NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso yar karbi 'yan APC zuwa NNPP

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya bayyana taron a matsayin babbar dama da ke nuna cewa 'yan APC sun yanke shawarar dawowa jam’iyyar NNPP.

Yayin da yake jawabi a taron da aka gudanar a gidansa da ke Kano, Kwankwaso ya ce:

“Na yi maraba da sababbin 'yan jam'iyya da suka dawo NNPP, kuma na sha alwashin cewa za a ba su cikakken adalci da hadin kai a tafiyarmu.”
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
'Yan APC sun sauya sheka zuwa NNPP Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

“Tsarin shugabanci na musamman a Kano da irin salon siyasa da muke da shi na kara jawo hankalin mutane da dama zuwa jam’iyyarmu, kuma ina karfafa gwiwar wadanda ke tunanin sauya sheka, su yi hakan ba tare da wata shakku ba.”

Kara karanta wannan

Yilwatda: Muhimman abubuwa game da sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

Ya karbi bayanin ne a yayin da ake ci gaba da alakanta Sanata Kwankwaso da wata ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, sai dai har yanzu babu bayani daga bangarorin biyu kan batun.

Jama’a na goyon bayan Kwankwaso

Magoya bayan Sanata Kwankwaso da dama sun bayyana goyon bayansu gare shi, inda suka bayyana shi a matsayin jagora nagari da kowa ke sha’awar bi.

Mustapha Rabiu ya wallafa cewa:

"Ba zan daina goyon bayan Rabiu Musa Kwankwaso har sai ya zama shugaban Najeriya."

Mohd Rabiu Adamu ya ce:

"Jagoran gaskiya daya tilo da ya rage wa Arewa a yanzu. Talakawa na tare da kai ranka ya dade."

El Malik Yunus ya rubuta cewa:

"Mai girma, al’amura sun kankama kuma jama’a sun shirya. Lokaci ne da za a sanya azama, ƙarfafa jagoranci da nufin ceto kasa."

Martanin fadar shugaban kasa ga Kwankwaso

A baya, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke zargin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Sunday Dare, ya fitar ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da muhimman ayyuka a Arewa.

Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyuka masu muhimmanci a fannonin sufuri, lafiya, noma da makamashi da gyaran titunan Abuja–Kaduna–Kano da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.