ADC Ta Yi Tone Tone, Ta Ce Akwai Baraka tsakanin Tinubu da Shettima

ADC Ta Yi Tone Tone, Ta Ce Akwai Baraka tsakanin Tinubu da Shettima

  • Ofishin Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da rashin kulawa da matsalolin tattalin arziki da na tsaro
  • Hadimin Atiku ya ce shugaban kasar yana rura wutar rikici a jam’iyyun adawa da amfani da hukumomin gwamnati don dakile su
  • 'Yan ADC sun gargadi Tinubu da ya daina shisshigi cikin harkokin jam’iyyar adawa, ya mayar da hankali kan wahalhalun ‘yan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ofishin yada labaran Atiku Abubakar ya fitar da wata sanarwa mai zafi da ke sukar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta bukaci Tinubu ya fi maida hankali kan gyaran kasa da tattalin arziki maimakon shisshigi cikin harkokin jam’iyyun adawa.

'Yan ADC sun zargi Tinubu da kokarin jefa musu rikici
'Yan ADC sun zargi Tinubu da kokarin jefa musu rikici. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga|Peter Obi
Source: Facebook

Sanarwar da Paul Ibe ya fitar a Facebook a madadin ofishin Atiku ta ce Tinubu na bata lokaci yana sukar 'yan adawa yayin da Najeriya ke fama da matsalolin tattali, rashin tsaro da yunwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin ADC kan alakar Tinubu, Shettima

Sanarwar ta ce kamata ya yi Bola Tinubu ya mayar da hankali kan warware sabanin da ke tsakanin shi da Kashim Shettima maimakon shiga maganar 'yan adawa.

Sun ce shisshigin da shugaban ke yi cikin 'yan adawa musamman ta hanyar amfani da kudin gwamnati wajen tayar da zaune tsaye ya zama babbar matsala da ke kara dagula siyasar kasar.

An zargi Tiubu da jefa rikici a ADC

Sanarwar ta ce rikicin da aka gani a tsakanin magoya bayan Atiku da Peter Obi a jam’iyyar hadakar adawa wani yunkuri ne daga fadar shugaban kasa domin haddasa rabuwar kai.

Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta ce:

“Shugaban kasa Tinubu ya fi maida hankali wajen bata jam’iyyun adawa ta hanyar rura wutar rikici a cikinsu, tare da amfani da kudin gwamnati domin rage karfin muryoyinsu.”

Sun kara da cewa wannan dabarar ba ta yi nasara ba, domin yanzu hadin kan jam’iyyun adawa ya kara karfi, kuma sun kuduri aniyar fuskantar gwamnatin da gazawa a matakai da dama.

Kara karanta wannan

Bayan taron daidaita farashin fetur, Shettima ya yi magana kan tallafin mai

Bola Tinubu da mataimakin shi, Kashim Shettima
Bola Tinubu da mataimakin shi, Kashim Shettima. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

ADC ta ce Tinubu ya gaza a shekaru 2

Sanarwar ta bayyana cewa a fiye da rabin wa’adinsa na farko, Tinubu bai nuna wata hanyar fita daga halin da kasar ke ciki ba.

“Gwamnatin APC mai mulki ba ta da hanyar fitar da Najeriya daga matsaloli, ba ta da hazaka, kuma ta yi biris da wahalhalun da al’ummar Najeriya ke ciki,”

- Inji sanarwar.

Ofishin Atiku ya ce maimakon shugaba Tinubu ya mayar da hankali wajen yaki da ‘yan bindiga a jihohin Benue, Zamfara, Neja da sauran su, sai ya dauki batun murkushe jam’iyyun adawa.

APC za ta yi maraba da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa sabon shugaban APC na kasa ya yi jawabi kan yanayin siyasar Najeriya bayan shan rantsuwa.

Sabon shugaban ya bayyana cewa a shirye suke su karbi madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso idan ya sauya sheka.

Baya ga Kwankwaso, shugaban ya ce APC ta bude kofofinta ga duk wani tsohon dan jam'iyyar da ya sauya sheka a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng