Tinubu Ya Fadi Sabon Aikin da Ganduje zai Yi wa APC a Matakin Kasa

Tinubu Ya Fadi Sabon Aikin da Ganduje zai Yi wa APC a Matakin Kasa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya soki jam’iyyar ADC da wasu ‘yan adawa, ya bayyana cewa suna cikin rudani
  • Bola Tinubu ya yabawa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje, kan kafa cibiyar nazarin cigaba a jam’iyyar
  • Ya ce gwamnatin sa na kokarin farfado da tattalin arzikin Najeriya da yaki da ‘yan ta’adda domin tabbatar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa jam’iyyar ADC, da wasu jiga-jigan adawa ke goyon baya yanzu, jam’iyya ce mai cike da rudani da rashin tsari.

Shugaban ya fadi hakan ne a wajen taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar APC karo na 14 da aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Ganduje ya aiko saƙo daga Landan kan naɗin sabon shugaban APC na ƙasa

Shugaban kasan Najeriya Bola Tinubu
Shugaban kasan Najeriya Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Bola Tinubu ya yi magana ne bayan an zabi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa a taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bayyana cewa ba laifi ba ne mutum ya bar jirgin da ke nutsewa kuma ya guji shiga cikin abin da ya kira ‘rudani’.

Wannan furuci nasa ya jawo martani daga jam’iyyar ADC da kungiyar CUPP da kuma Paul Ibe, da yake magana da yawun Atiku Abubakar.

Wane aiki Ganduje zai yi wa APC?

Shugaba Tinubu ya mika godiyarsa ga tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, bisa irin rawar da ya taka a lokacin da yake jagorancin jam’iyyar.

Bola Tinubu ya ce ya ba Ganduje aiki na kafa cibiyar nazarin cigaba a jam’iyyar APC kuma ya kammala wannan aiki.

Ya kara da cewa sakataren jam’iyyar zai hada kai da sabon shugaban don farfado da wannan cibiya, tare da yiwuwar ci gaba da amfani da Ganduje a matsayin mai ba da shawara.

Kara karanta wannan

2027: Sabon shugaban APC ya yi magana kan yiwuwar sauya shekar Kwankwaso

Shugaban kasar ya bayyana cewa an dage ranar zaben jam’iyyar daga matakin jihohi zuwa kananan hukumomi da gundumomi zuwa watan Disamba.

Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Ya ce wannan dama ce ta karfafa jam’iyyar da kara hada kai da jama’a, yana mai cewa kofa a bude take ga duk wanda ke son shiga cikin tafiyar.

Maganar Tinubu kan tattali da tsaro

Punch ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya yana farfadowa a hankali duk da kalubalen da ke tattare da hakan.

Bola Tinubu ya ce gwamnati na aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, kuma yanzu ana ganin haske.

Dangane da tsaro, ya ce an samu ci gaba wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga inda ya bayyana cewa an hallaka dubban ‘yan ta’adda.

Sai dai duk da haka, shugaban kasar ya gargadi gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki da kada su yi sakaci.

Hakeem Baba ya gargadi Tinubu kan 2027

A wani rahoton, kun ji cewa dattijon Arewa, Hakeem Baba Ahmed ya gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sauka, Yilwatda ya hau: Jerin shugabannin APC 9 daga 2013 zuwa 2025

Hakeem Baba ya bukaci shugaban kasar da ya mayar da hankali kan ayyukan cigaba maimakon harkokin siyasa da zabe.

Ya bayyana cewa 'yan Najeriya za a iya kifar da Bola Tinubu a zaben 2027 matukar bai cika alkawarin da ya musu a 2023 ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng