Ganduje Ya Aiko Saƙo daga Landan kan Nadin Sabon Shugaban APC na Ƙasa
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban APC
- Ganduje, wanda ya yi murabus daga shugabancin APC, ya ce naɗin ya zo a lokacin da ya dace domin ciyar da jam'iyyar mai mulki zuwa gaba
- Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cikakken goyon bayansa ga sabon shugaban APC, yana mai cewa ya gamsu da kwarewa da hikimarsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba da nadin Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa.
Ganduje, wanda yanzu haka yake Landan a ƙasar Burtaniya, ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa zaƙulo wanda ya dace ya shugabanci jam'iyyar APC.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba Ganduje ya ajiye muƙamin shugaban APC na ƙasa a farkon watan Yuli da muke ciki bisa dalilin rashin lafiya kamar yadda ya bayyana a wasiƙarsa.
Ganduje ya yaba da naɗin sabon shugaban APC
Da yake martani kan naɗa magajinsa, Ganduje ya bayyana naɗin Farfesa Yilwatda a matsayin wata dabara da ta zo a lokacin da ya dace.
Tsohon Gwamnan Kano ya nuna gamsuwa matuƙa da ƙwarewa, basira, gogewar shugabanci da haƙurin sabon shugaban PDP, wanda ya ce zai ciyar jam'iyyar zuwa gaba.
Haka kuma, Ganduje ya yi amfani da damar wajen yaba wa Kwamitin Zartarwa na APC (NEC) da sauran sassan jam'yyar bisa yadda suka gudanar da tsari na gaskiya da fahimtar juna wajen naɗa Farfesa Yilwatda.
Dr. Ganduje ya bukaci sabon shugaban APC da ya ɗora daga inda ya tsaya, kamar yadda shi ma ya ɗora daga nasarorin da magabacinsa, Sanata Abdullahi Adamu, ya samar.
Ganduje ya miƙa godiya ga Shugaba Tinubu
Ya kuma godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima saboda rawar gani da hikimar da suka nuna wajen jagorantar APC a irin wannan lokaci da aka samu sauyin shugabanci.
“Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa sun sake nuna ƙwarewa da hangen nesa a harkokin jam’iyyarmu mai girma. Kokarinsu wajen tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin APC abin yabawa ne.
"Kuma ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su goyi bayan sabon shugaban APC domin aiwatar da manufar 'Sabunta Fata' ta Shugaban Ƙasa. Ina tabbatar wa Farfesa Yilwatda da cikakken goyon baya na.
"Ina kira ga shugabanni, gwamnoni, ‘yan majalisa da duka ƴan APC a faɗin ƙasa da su tsaya a bayansa, su ba shi goyon baya don ya cika manufofin jam’iyyarmu na gina dandalin haɗin kai, ci gaba ga ƴan Najeriya.
- Dr. Abdullahi Ganduje.

Source: Twitter
Sabon shugaban APC ya faɗi shirinsa
A baya, kun ji cewa sabon shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa zai ɗauki matakai masu tsauri domin kawo cu gaba mao ɗorewa a jam'iyya.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai fara neman shawara da sassa daban-daban na jam’iyyar gabanin ya ɗauki matakai masu tsauri don amfaninta.
Shugaban na APC ya ce zai yi shirye-shirye da aiki tukuru domin jawo wasu gwamnonin PDP da na sauran jam’iyyun adawa zuwa inuwar jam'iyya mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


