Nentawe: Sabon Shugaban APC Ya Fadi Salon Mulkin da Zai Yi a Jam'iyyar

Nentawe: Sabon Shugaban APC Ya Fadi Salon Mulkin da Zai Yi a Jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin shugabanta na ƙasa
  • Farfesa Nentawe ya bayyana cewa ba zai yi wasa wajen ɗaukar matakan da suka dace domin ci gaban jam'iyyar APC
  • Hakazalika ya nuna cewa zai yi ƙoƙari sosai wajen raunata jam'iyyun adawa ta hanyar jawo gwamnoninsu zuwa cikin APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sabon shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sha alwashi kan irin shugabancin da zai yi.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya sha alwashin ɗaukar matakai masu tsauri a matsayinsa na jagoran jam’iyyar APC mai mulki.

Nentawe ya zama shugaban APC
Nentawe Yilwatda zai dauki matakai masu tsauri a APC Hoto: @ImranMuhdz
Asali: Twitter

Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Alhamis, 24 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban APC ya faɗi shirinsa

An yi hira da shi ne dai awanni bayan bayyana shi a hukumance a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC a Abuja.

Kara karanta wannan

Nentawe: Alkawuran da shugaban APC ya daukar wa jamiyya bayan tafiyar Ganduje

"Goyon bayan da suke yi min na nufin su tabbatar da cewa ina ɗaukar matakai masu tsauri amma cikin ladabi da aiki tare, don amfanin jam’iyya baki ɗaya."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Nentawe Yilwatda, wanda ya kwatanta halinsa na sauƙin kai da na Shugaba Bola Tinubu, ya ce zai yi shawara da sassa daban-daban na jam’iyyar sannan ya ɗauki matakai masu tsauri don amfaninta.

“Tabbas zan yi hakan, domin kuwa haka shugaban ƙasa ya buƙaci na yi, kuma ƴan jam’iyya ma suna bukatar hakan daga gare ni"
"Ka kalli yadda shugaban ƙasa yake, mai magana da sauƙi, mai natsuwa, mai ladabi amma dubi inda yake kai ƙasar: yana ɗaukar matakai masu tsauri da mutane ma suna jin tsoron su yi magana a kansu."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Nentawe Yilwatda zai farauci gwamnonin PDP

Sabon shugaban na APC ya ce zai yi shirye-shirye da aiki tukuru domin jawo wasu gwamnonin PDP da na sauran jam’iyyu masu hamayya zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yilwatda: Muhimman abubuwa game da sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

"Aiki na shi ne haɗa kan jam’iyya, da kuma faɗaɗa jam’iyya. Muna da gwamnoni 23, kuma har yanzu muna ƙaruwa. Aiki na shi ne ƙara jawo wasu. Za mu yi shirye-shirye mu jawo wasu."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Nentawe zai fara aiki a shugabancin APC
Nentawe Yilwatda zai jawo gwamnonin PDP zuwa APC Hoto: Prof. Yilwatda Nentawe
Asali: Twitter

Yilwatda ya bayyana cewa ƙwarewarsa a matsayin injiniya, tsohon malami a jami’ar moma ta tarayya da ke Makurdi, jihar Benue, tsohon kwamishinan hukumar INEC, da kuma Ministan harkokin jinƙai za su taimaka masa.

Ya ce ƙwarewar da ya samu ta sanya ya samu gogewar da ake buƙata wajen taka babbar rawa a matsayin shugaban jam’iyya na ƙasa.

Tinubu ya ba gwamnonin APC shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tunatar da gwamnonin jam'iyyar APC.

Mai girma Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin da su ƙara tashi tsaye wajen yi wa mutanen da ke ƙarƙashinsu abubuwan da suka dace.

Shugaban ƙasan ya nuna cewa wasu ƴan Najeriya na ƙorafi kan rashin morar romon dimokuraɗiyya a gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng