"An Yi Watsi da Arewa," Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu, Ya Faɗi Kalamai Masu Ɗaci

"An Yi Watsi da Arewa," Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu, Ya Faɗi Kalamai Masu Ɗaci

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu kan abin da ya kira watsi da Arewacin Najeriya
  • Kwankwaso ya zargi gwamnati mai ci da karkatar da hankalinta wajen gina yankin Kudu da albarkatun ƙasar nan
  • Ya ce titunan Arewa sun lalace matuƙa, inda ya shawarci shugaban ƙasa ya yi adalci wajen raba albarkatu tsakanin Arewa da Kudu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jagoran siyasar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya kira watsi da yankin Arewacin Najeriya.

Kwankwaso ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da dukiyar ƙasa wajen aiwatar da ayyukan ci gaban yankin Kudu inda shugaban ƙasar ya fito.

Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Jagoran NNPP na ƙasa ya faɗi haka ne a taron masu ruwa tsaki da aka shirya don tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa ranar Alhamis a Kano, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

'An buga an bar mu,' Kwankwaso ya faɗi abin da ya sa Kwankwasiyya ta gagara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

Kwankwaso ya ce:

"Muna ba Gwamnatin Tarayya shawara ta gyara yadda ake raba tattalin arzikin kasa. Daga bayanan da muka samu, kasafi mai tsoka yana tafiya ne zuwa ɓangare guda na kasar nan.”

Kwankwaso, wanda ya yi takarar shugabancin ƙasa a 2023 a inuwar NNPP, ya zargi APC da rashin adalci wajen raba albarkatun ƙasa tsakanin Kudu da Arewa.

“Ina baku shawara masu kokarin kwace komai da ƙarfi da yaji ku sani matsalolin da muke fama da su, suna da alaƙa da rashin isassun albarkatu da kuma wawure ɗan wanda muke da shi.
“Wannan ya sa matsalar tsaro, da talauci da sauransu suka mana katutu. Haka na faruwa ne a nan Arewa, amma kamar hamada ce, zai yadu zuwa ko’ina,” inji shi.

Kwankwaso ya koka kan taɓarɓarewar Arewa

Tsohon gwamnan ya ce galibin titunan Arewa sun lalace matuka, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware kuɗaɗen manyan ayyuka a yankin Kudu.

Kara karanta wannan

Minista ya soki Kwankwaso da ya taba Tinubu, ya masa gorin ƙuri'un Buhari miliyan 12

“Jiya, na so biyo jirgi, amma aka canza lokacin tashin jirginmu daga ƙarfe 3:00 na yamma zuwa 8:00 na dare. Bisa dole na taho a mota daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, tafiya a wannan titin azaba ce.
"Titin ya lalace matuka. Wannan titi ne da aka fara shekaru da dama da suka gabata tun daga farkon mulkin APC. Yanzu ana gaya mana cewa za a yi sabon titi daga Kudu zuwa Gabas.
"Muna goyon bayan gina ababen more rayuwa ko’ina a ƙasar nan, zai amfani talakawa. Amma halin da ake ciki gwamnati na karkatar da dukiyar ƙasa zuwa yanki guda a ƙasar nan.

- Rabiu Musa Kwannwaso.

Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta canza alkibla, ta yi wa kowane yanki adalci a Najeriya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta sauya akalarta don tabbatar da adalci wajen rabon albarkatun ƙasa tare da tafiya da kowane yanki na ƙasar, rahoton Daily Trust.

Wani ɗan Kwankwasiyya, Sanusi Isiya ya shaidawa Legit Hausa cewa duk ɗan Arewa matuƙar ba son zuciya zai sa ba, ya san maganar Kwankwaso gaskiya ce.

A cewarsa, duk waɗanda ya kamata su fito su gaya gwamnatin gaskiya ba za su iya ba saboda suna amfana da ita ko kuma suna da wani buri na son rai a zukatansu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ballo aiki, kungiyar Yarbawa ta yi masa raddi kan sukar Tinubu

Sanusi ya ce:

"Ni banga abin surutu kan kalaman maigida ba, kowa ya san Arewa ita ce koma baya, da yawan masu sukar Kwankwaso ba su san abin da ya sani ba, ko kuma son zuciya.
"Ya zama dole manyan Arewa su tashi tsaye, idan ba haka ba, ba abin da Arewa za ta samu a wannan gwamnatin, za a ci gaba da barinmu a baya."

Kwankwaso zai iya maye gurbin Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Malam Aminu Ringim ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasan da zai iya gaje farin jinin marigayi Muhammadu Buhari.

Jigon NNPP ya haɗa Kwankwaso da jagororin Arewa kamar Sir Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen kare talakawa.

Ya ƙara da cewa Kwankwaso bai fito a matsayin ɗan siyasa na masu hannu da shuni ba, sai dai mutum ne mai sauƙin kai, mai shiga talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262