Yilwatda: Muhimman Abubuwa game da Sabon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa

Yilwatda: Muhimman Abubuwa game da Sabon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa

Jam’iyya mai mulki ta APC ta shiga sabon matakin jagoranci bayan da ta zaɓi Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – An zabe shi ne a ranar 24 ga Yuli, 2025, bayan murabus da tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi bisa dalilan rashin lafiya.

Sabon shugaban APC na ƙasa, Yilwatda
APC ta zaɓi sabon shugabanta na ƙasa Hoto: @Imranmuhdz/All Progressives Congress
Asali: Twitter

Legit ta tattaro muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon shugaban jam’iyya mai mulki a Najeriya.

1. Asali da karatun sabon shugaban APC

Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X cewa an haifi Farfesa Nentawe Yilwatda a ranar 8 ga Agusta, 1968.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haife shi a unguwar Dungung, cikin karamar hukumar Kanke, Filato ga iyalin babban jagoran Kirista, marigayi Rabaran Toma Yilwatda.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Yilwatda ya samu goge wa ta a fannonin ilimi daban-daban da suka hada da; Digiri na farko a fannin Injiniyan Lantarki daga Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Makurdi a shekarar 1992.

Sabon shugaban ya samu digiri na biyu a jami'ar ATBU da ke jihar Bauchi, sai kuma digirin digirgir (PhD) daga Jami’ar Nsukka.

2. APC: Ayyukan da Yilwatda ya yi kafin yanzu

Baya ga karatu da koyarwa, Yilwatda ya taka rawa sosai a fannin gwamnati da ci gaban al’umma.

Imran Muhammad ya wallafa a shafin X cewa sabon shugaban APC ya rike mukamin Kwamishinan Zaɓe na INEC a jihar Binuwai daga Yuli 2017 zuwa Disamba 2021.

APC ta kawo ƙarshen sa rai da kujerar shugabanta da wasu ke yi
Muhimman abubuwa game da Yilwatda Hoto: All Progressives Congress
Asali: Twitter

A tsakanin wannan lokaci, ya jagoranci zabuka a jihohi biyar, daga cikinsu akwai Anambra, Osun, Cross River, da Ribas.

Ya yi aiki a matsayin kwararre/mai ba da shawara na kimiyya da fasaha ga kungiyoyi na ƙasa da na duniya kamar UNICEF, Bankin Duniya, Tarayyar Turai (EU), da TECHVILE USA tsawon fiye da shekaru 29.

Kara karanta wannan

Siyasa: Rikici ya yi kamari a SDP, an tura mutanen El Rufa'i kurkuku

3. Siyasa da tasirin Yilwatda a APC

Bayan barin INEC a shekarar 2021, Yilwatda ya shiga siyasa kai tsaye, inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Filato a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Kodayake bai yi nasara ba, sai dai ya taka muhimmiyar rawa a yi wa na Shugaban ƙasa Bola Tinubu/Kashim Shettima kamfe a jihar Filato.

4. Nada shi minista bayan rasa gwamna

A cikin Oktoba 2024, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shi a matsayin Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, inda ya jagoranci muhimman shirye-shiryen jinƙai.

Farfesan ya karbi matsayin ne bayan kotun daukaka kara ta ba shi nasara a kan PDP a zaben gwamnan Filato da aka yi a 2023.

Shi ne ya canji Betta Edu wanda shugaban kasa ya dakatar bisa zargin aikata ba daidai ba.

5. Iyali da sauran bayani game da Yilwatda

Farfesa Nentawe Yilwatda ya auri Dr. Martina Yilwatda Goshwe, kuma Allah ya albarkace su da yara, ciki har da ɗansu, Beji Nentawe Goshwe.

Kara karanta wannan

Jim kadan da nadin shugabanta na kasa, APC ta yi sababbin sauye sauye a NWC

Suna zaune a Rayfield, cikin karamar hukumar Jos ta Kudu, a jihar Filato, kuma an bayyana shi da mai haba-baba da ƴan uwa da abokan arziki.

APC ta zaɓi sabon shugabanta na ƙasa

A baya, mun wallafa cewa a ranar 24 ga Yuli, 2025, kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na APC ya tabbatar da nadin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Zaben Farfesa Yilwatda ya biyo bayan murabus da Abdullahi Umar Ganduje ya yi daga jagorancin jam’iyyar tun bayan babban zaben 2023 zuwa shekarar 2025.

Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda kwararren masanin kimiyyar lantarki ne daga Filato, kuma tsohon ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin APC a jihar a lokacin zaɓen 2023..

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng