'Kwankwaso na Tsaka Mai Wuya a Siyasa tsakanin Shiga APC, PDP ko ADC,'
- Ana ganin Rabiu Kwankwaso na fuskantar kalubale wajen yanke matsaya tsakanin komawa APC ko shiga kawancen ADC
- Masana na cewa NNPP ba ta da karfin da za ta iya lashe zaben shugaban kasa domin ba ta da karfi a matakin kasa baki daya
- A kan haka ake ganin kowace hanya da Kwankwaso zai bi tana dauke da haduran siyasa da za su iya shafar shi kai tsaye
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, na fuskantar muhimmin mataki a tafiyar siyasarsa.
Taron da ya halarta a fadar shugaban kasa da rade-radin haduwa da shugaba Bola Tinubu ya kara janyo hasashe kan yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP.

Source: Twitter
Daya daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu kan batun shi ne Dr. Yakubu Sani Wudil, wanda ya fitar da bayani kan siyasar Kwankwaso a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ake ci gaba da hasashe, ra’ayoyi da dama sun bayyana kan makomar Kwankwaso da irin hanyoyin da zai iya bi a siyasarsa ta gaba.
Wasu na ganin yana da damar daukar sabon salo yayin da wasu ke cewa duk wata hanyar da zai bi ba za ta rasa illoli ba.
'NNPP ba ta da karfi a kasa,' Dr Wudil
A cewar Dr. Wudil, Kwankwaso ya samu kansa a cikin mawuyacin hali na siyasa, kuma zabin da ke gabansa ba su da sauki.
Ya ce jam’iyyar NNPP da Kwankwaso ke ciki yanzu ba ta da karfin da za ta iya lashe zabe a matakin kasa.
Hakan ya sa Dr Wudil cewa Kwankwaso na da zabi biyu ne kacal a halin da siyasar kasar ta nuna a yanzu.

Kara karanta wannan
Janar Tukur Buratai ya tsage gaskiya, ya fadi abin da ke shigar da matasa ta'addanci
Ya ce ko dai ya hade da jam’iyyar APC mai mulki ko kuma ya shiga kawance da jam’iyyar ADC, kowanne daga cikin wadannan hanyoyi, a cewarsa, yana da illolinsa.
Wudil ya fadi kalubalen shiga ADC
Idan ya zabi shiga kawancen ADC, Dr. Wudil ya ce akwai yiyuwar karancin damar samun tikitin shugaban kasa.
Ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar wani dan Arewa ne zai samu tikitin a maimakon Kwankwaso.
Ya ce ko da ADC ta samu nasarar lashe zabe, akwai yiwuwar mulki zai koma Kudu a zaben na gaba saboda karba-karba tsakanin Arewa da Kudu, lamarin da zai dakile burin Kwankwaso.
Ya dace Kwankwaso ya koma APC?
A daya hannun kuma, idan Kwankwaso ya koma jam’iyyar APC, Dr Wudil wannan zai iya janyo masa fushin magoya baya.
Dr. Wudil ya ce hakan zai sa wasu su dauka cewa ya mika wuya ga burin karan kansa, domin ya taba sukar APC da shugabanninta a baya.
Haka kuma, komawa APC na iya haifar masa da koma baya a tushe, inda magoya bayansa ke iya jin an yaudare su.
Duk da wannan tsinkaye da fashin baki, Dr. Wudil ya ce har yanzu akwai damar abubuwa su canza bisa la’akari da sauye-sauyen da ke faruwa a siyasar Najeriya.

Source: Twitter
Dan Bello na rikici da 'yan Kwankwasiyya
A wani rahoton, kun ji cewa Bello Galadanci da aka fi sani da 'Dan Bello ya yi magana kan yanayin tafiyar siyasar Kwankwasiyya.
'Dan Bello ya zargi 'yan Kwankwasiyya da mika wuya ga wani mutum daya maimakon saka wani buri na kawo sauyi a gaba.
Sai dai 'yan Kwankwasiyya sun masa martani suna kallon kamar bai fahimci yadda tarihin gwagwarmaya ke tafiya a duniya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

