Bayan Tafiyar Atiku, PDP Ta Fara Hangen Wanda Za Ta Tsayar Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

Bayan Tafiyar Atiku, PDP Ta Fara Hangen Wanda Za Ta Tsayar Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

  • Ƙungiyar waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP a 1998 sun bayyana matsayarsu kan wanda ya kamata a tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
  • A wani taro da suka gudanar a Abuja, jiga-jigan PDP sun amince a ɗauko ɗan takara a Kudancin Najeriya domin tabbatar da adalci da daidaito
  • Farfesa Jerry Gana ya caccaki gwamnatin APC da cewa ta kawo talauci dabrashin tsaro maimakon alkawarin da ta yi na kawo canji a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyar waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP ta amince da ɗauko ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudancin Najeriya a zaben 2027 mai zuwa.

A cewarta, wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen dawo da ainihin manufofin jam’iyyar PDP na adalci, daidaito da haɗin kan ƙasa.

Taron masu ruwa da tsaki a PDP.
Shugabannin PDP sun yanke yankin da za a ba takarar shugaban ƙasa a zaben 2027 Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Ta bayyana hakan ne a wurin taron kasa na iyayen jam'iyyar PDP da aka gudanar a Abuja jiya Laraba, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Wane yanki PDP za ta ɗauko ɗan takara a 2027?

Farfesa Jerry Gana, tsohon Ministan Yaɗa Labarai kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP, ya jaddada bukatar miƙa tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa Kudu.

Wasu daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki; Gwamnan Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed; da tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu.

Da yake jawabi, Jerry Gana ya ce:

“Bisa la'akari da hangen nesan waɗanda suka kafa PDP, muna roƙon dukkan shugabannin PDP su goyi bayan miƙa tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa Kudancin ƙasar nan.
"Wannan hanya ba wai kawai za ta taimaka mana wajen samun nasara ba ne kaɗai, har ila yau za ta karfafa adalci da gaskiya.”

PDP ta tuna aikin da ta yi a Najeriya tun 1999

Ya ƙara da cewa har yanzu PDP na nan a raye kuma tana ƙoƙarin haɗa kai domin ceto Najeriya daga gazawar jam’iyyar APC, musamman a fannin tsaro, tattalin arziki da haɗin kan ƙasa, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fito fili ya fadi wadanda suka assasa matsalolin jam'iyyar

“Bari na tuna maku, PDP ce ta gina muhimman hukumomi kamar EFCC, ICPC, UBEC da TETFund. Mu ne muka daidaita dimokuraɗiyya, muka bunƙasa tattalin arziki.
"Yanzu lokaci ne da zamu tsara manufofin ceto Najeriya. Ƴan Nigeriya na fuskantar tsananin talauci, rashin tsaro da rashin fata fiye da kowanne lokaci.
"APC ta yi alƙawarin canji, amma abin da suka kawo shine sarƙoƙi. Sarƙoƙin wahala, talauci da rashin fata.

- Farfesa Jerry Gana.

Farfesa Jerry Gana.
Jerry Gana ya ce PDP ba ta mutu ba, kuma za ta dawo kan ganiyarta Hoto: @RealJerryGana
Source: Twitter

Damagum ya gano tushen matsalar PDP

A baya, kun ji cewa muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum ya ce PDP tana fama da matsaloli ne saboda mambobinta sun yi watsi da manufofi da aƙidunta na asali.

A cewarsa, a yanzu ƴan PDP sun fi maida hankali kan burinsa na neman mulki, wanda hakan ya zama tushen rikici da samun matsaloli daban-daban.

Damagum ya ƙara da cewa za su iya warware duk wata damuwa idan har ƴaƴan PDP suka fara fifita muradan PDP fiye da bukatarsu ta kai da kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262