Damagum: Shugaban PDP Ya Fito Fili Ya Fadi Wadanda Suka Assasa Matsalolin Jam'iyyar

Damagum: Shugaban PDP Ya Fito Fili Ya Fadi Wadanda Suka Assasa Matsalolin Jam'iyyar

  • Shugaban riƙo na PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya fito ƴa yi magana halin da jam'iyyar ta tsinci kanta a ciki
  • Ambasada Umar Damagum ya kawar da batun ɓoye-ɓoye ya gayawa mambobin jam'iyyar gaskiya kan halin da ake ciki
  • Shugaban na PDP ya nuna cewa ƴaƴan jam'iyyar ne da kansu suka jefa ta cikin matsalolin da suka daɗe suna addabarta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagum, ya yi magana kan matsalolin da suka addabi jam'iyyar.

Umar Damagum ya ce jam’iyyar PDP tana fama da matsaloli ne saboda mambobinta sun yi watsi da manufofi da aƙidunta, suka fifita son zuciya da buri na ƙashin kansu.

Damagum ya magantu kan rikicin PDP
Damagum ya tabo batun rikicin PDP Hoto: Musa Mohammed Kaska
Source: Twitter

Jam'iyyar PDP ta yi taro a Abuja

Shugaban na PDP ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a ranar Laraba a birnin Abuja, wanda ya haɗa da mambobin da suka kafa jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Ficewar Atiku ta fara kawo alheri, tsohon ɗan takarar shugaban kasa ya koma PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashar Arise ta ce Damagum ya bayyana rikice-rikicen cikin gida da PDP ke fuskanta a matsayin “ciwon da muka jawo wa kanmu da kanmu,” yana fatan cewa waɗanda suka bar jam’iyyar za su “fahimci kuskurensu" daga bisani su dawo.

Damagum ya gargadi ƴan jam’iyyar da su daina ɓata sunan PDP da kuma cuɗanya da wasu jam’iyyun siyasa.

Me Damagum ya ce kan matsalolin PDP?

"Kai ɗan PDP ne ko ba haka ba, domin ba za ka iya kasancewa cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda ba".
"Amma dole mu fuskanci gaskiyar magana, mafi yawan raunin da PDP ke fama da shi, mun jawo wa kanmu ne da kanmu. Tun daga zamanin Obasanjo har zuwa yau, mun fi yawan yin watsi da aƙida saboda son zuciya da burin ƙashin kanmu."
"Hakan ya jawo mana asara sosai. Amma duk da haka, har yanzu akwai wata kyakkyawar ƙima da PDP ke da ita. Dabarun da muka kafa jam’iyyar da su, ƙudurin mu kan dimokuradiyyar cikin gida, hanyoyin da muke amfani da su wajen sasanci da warware rikice-rikice."

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya yi murabus daga PDP a zungureriyar wasikar shafi 9

“Waɗannan ba abubuwa ne na yau da kullum ba. Sune tubalin da suka gina PDP, suka kuma tabbatar da ita a matsayin ginshiƙin tafiyar dimokuradiyyar Najeriya, kuma har yanzu sune ƙarfinmu da muke dogara da su."
“Amma, a sani, ko wane lokaci, ƙofarmu a buɗe take ga waɗanda suke son komawa jam’iyyar. Kuma addu’ata ita ce, idan sun dawo, za su sake gano kansu."
"Daga ƙarshe dai, PDP ce jam’iyyar da ta samar da mafakar siyasa ta farko ga mutane da dama."

- Umar Damagum

Umar Damagum ya ba da shawara kan rikicin PDP
Damagum na fatan wadanda suka fice PDP su dawo Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa raunin da suka jawo wa kansu a jam’iyyar yana iya warkewa, idan suka daina fifita buƙatun kai suka maida hankali kan na jam'iyya.

Olawepo Hashim ya koma PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, Gbenga Olawepo Hashim ya koma jam'iyyar PDP.

Olawepo Hashim ya koma PDP ne bayan ya raba gari da babbar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa PDP ce jam'iyyar da za ta iya ceto Najeriya duk kuwa da matsalolin da take fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng