'Dan Bello Ya Zafafa Harshe kan Kwankwaso, Ya Fara Rikici da 'Yan Kwankwasiyya

'Dan Bello Ya Zafafa Harshe kan Kwankwaso, Ya Fara Rikici da 'Yan Kwankwasiyya

  • Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello, ya bayyana cewa Kwankwasiyya na fama da rashin shugabanci da akida mai ma’ana
  • Ya ce duk da yawan matasa da ke cikin tafiyar, an mayar da su bayi ga mutum daya, ba ga manufofi na siyasa da cigaba ba
  • 'Yan Kwankwasiyya sun mayar da martani mai zafi a gare shi, inda Dan Bello ya nemi su janye kalamansu cikin sa'o'i 12 masu zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Dan gwagwarmaya, Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello, ya furta kalamai game da tsarin tafiyar Kwankwasiyya da suka tayar da kura.

Dan Bello ya bayyana cewa matsalar Kwankwasiyya ba yawan mambobi ba ne, illa dai rashin ingantaccen shugabanci da akida.

Kara karanta wannan

Dukan Islamiyya ya jawo babbar matsala, fitaccen ɗan TikTok ya bar addinin Musulunci

Rikici ya barke tsakanin Dan Bello da 'yan Kwankwasiyya
Rikici ya barke tsakanin Dan Bello da 'yan Kwankwasiyya. Hoto: Dan Bello|Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dan Bello ya zargi Kwankwasiyya da karkata daga manufofin ci gaban jama’a zuwa bautar mutum daya.

'Yan Kwankwasiyya sun mayar masa da martani mai zafi, lamarin da ya sa Dan Bello ya fitar da sabuwar sanarwa yana gargadin su su janye kalamansu cikin sa'o’i 12.

Zargin 'Dan Bello kan tafiyar Kwankwasiyya

'Dan Bello ya ce siyasar Kwankwasiyya a yanzu ba ta dauko hanyar cigaba ba, A cewarsa, ta zama kungiya mai yaɗa gumurzu.

Ya kara da cewa:

“Sun mallaki dimbin matasa masu kuzari, amma an tsare su a cikin siyasar bauta: bauta ga mutum guda, ba ga manufa ba.”

A cewarsa, wanda ke da akida ko tunani daban da na tafiyar, ana kallonsa a matsayin abokin gaba ko mai cin amanar tafiya.

Kiran 'Dan Bello ga 'yan Kwankwasiyya

Dan Bello ya bukaci 'yan Kwankwasiyya da su farka daga bauta da kuma mafarkin cika burin mutum daya, su koma mafarkin cika burin al'umma.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan Yobe zai fita daga APC zuwa ADC, hadiminsa ya yi magana

Ya ce siyasa ba ta mutum daya ba ce, sai dai ya ce siyasa mai kyau ita ce gyaran rayuwar al’umma da tabbatar da walwala.

A cewarsa,

“Siyasa ba ta mutum ɗaya bace — siyasa ce ta gyara asibitoci, ta dawo da ilimi, ta kawo karshen yunwa da daukaka martabar ‘yan ƙasa.”

Ya kammala da cewa:

“Idan juyin juya hali ya tsaya a kan mutum guda, to bariki ne, ba sauyi ba.”
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Martanin Kwankwasiyya da gargadin Dan Bello

Bayan wannan furuci, ‘yan Kwankwasiyya da dama sun mayar da martani mai tsauri ga Dan Bello a kafafen sada zumunta.

Abdulaziz T. Bako ya wallafa a Facebook cewa:

"Maganar Ɗan Bello ta cewa wai juyin juya hali ba a yinsa a ƙarƙashin inuwar mutum ɗaya, magana ce da ta bayyana rashin fahimtarsa da tarihin sauyi da juyin juya hali.
"Kusan duk wani sauyi da juyin juya hali da aka samu a duniya an same shi ne ta hanyar yarda da wani shugaba guda ɗaya tal, tare da sallama masa amanar shugabanci da jagoranci."

A wani sakonsa na baya-bayan nan, Dan Bello ya zarge su da nuna hali da rashin karɓar shawara mai amfani.

Kara karanta wannan

Ana hasashen nasarar Tinubu a 2027 bayan haduwa da Kwankwaso a Aso Villa

Ya ce:

“Daga bai wa ‘yan Kwankwasiyya shawara mai kyau, sun fara nuna hali. To ina ba su shawara su janye kalamansu baki daya a cikin awa 12 ko kuma mu tafi mataki na gaba.”

Kwankwaso ya gana da 'yan NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da 'yan majalisar NNPP a Abuja.

Duk da cewa ba a gano abin da suka tattauna ba, ana hasashen sun tattauna wasu batutuwa ne da suka shafi siyasar Najeriya.

Kwankwaso ya gana da 'yan majalisar ne bayan ya hadu da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng