Ana Rade Radin Gwamnan Yobe Zai Fita daga APC zuwa ADC, Hadiminsa Ya Yi Magana
- Gwamnatin jihar Yobe ta ce rade-radin cewa Gwamna Mai Mala Buni zai koma jam’iyyar ADC karya ce marar tushe
- Hadimin gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana cewa wannan zance jita-jita ce da aka riga aka karyata a baya
- Wannan na zuwa ne yayin da APC ke shirin zaben sabon shugaban jam’iyya bayan murabus din Abdullahi Umar Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta karyata rade-radin da ke yawo cewa Mai Mala Buni yana shirin barin jam’iyyar APC domin komawa jam’iyyar ADC.
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin yin taron jam'iyyar APC na NEC inda ake sa ran zaben sabon shugaban jam'iyya.

Source: Facebook
Daraktan yada labarai da hulda da kafafen watsa labarai na gwamnan, Mamman Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Punch a Damaturu ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mamman Mohammed ya ce wannan jita-jita ba sabuwa ba ce, kuma tun da farko an riga an karyata ta, don haka ba ta da wata hujja.
Gwamna Buni ya ce ba zai shiga ADC ba
A cewar Mamman Mohammed, batun cewa Mai Mala Buni zai bar jam’iyyar APC karya ce, kuma maganar ba ta da tushe balle makama.
Ya ce:
“Wannan mafarki ne kawai. Wani ya taba yada irin wannan jita-jita a baya kuma mun riga mun karyata ta. Wannan zance babu gaskiya a cikinsa.”
Gwamna Buni na kishin jam’iyyar APC
Mamman ya bayyana cewa Gwamna Buni, wanda ya ke wa’adi na biyu a matsayin gwamna a karkashin jam’iyyar APC, ba zai zama wanda zai fice daga jam’iyyar ba.
Ya ce irin wannan zargi bai dace da mutum mai kima da biyayya ga jam’iyya kamar Gwamna Buni ba, don haka masu yada irin wannan magana su dinga yin taka-tsantsan.
APC na shirin taron NEC a Abuja
An fara yada jita-jitar ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke shirye-shiryen taron da za ta gudanar don zaben sabon shugaban jam’iyya a Abuja.
Taron na zuwa ne bayan murabus da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a watan da ya gabata saboda rashin lafiya.
A gefe guda kuma, wasu ‘yan adawa na kokarin hada kai karkashin jam’iyyar ADC domin fuskantar zaben 2027 da nufin kada Shugaba Bola Tinubu.

Source: UGC
Duk da haka, jam’iyyar APC ta bayyana cewa za ta ci gaba da mulki har bayan 2027, tare da niyyar lashe zabukan da ke tafe.
A wannan yanayi ne jita-jita ke yaduwa game da sauyin jam’iyya, musamman daga manyan ‘yan siyasa.
2027: Hakeem Baba Ahmad ya gargadi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimi a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
ADC: Atiku da El Rufai sun fara fuskantar abin da ba su yi tsammani ba daga manyan Arewa
Rahotanni sun bayyana cewa Hakeem Baba ya ce ya kamata shugaban kasar ya mayar da hankali a kan cigaban kasa maimakon harkokin siyasa.
Ya kuma kara da cewa 'yan Najeriya suna da damar kifar da Bola Tinubu idan bai gamsar da su a shekara hudu na farko da ya yi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

