Ficewar Atiku Ta Fara Kawo Alheri, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma PDP

Ficewar Atiku Ta Fara Kawo Alheri, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma PDP

  • Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, ya koma jam'iyyar PDP bayan tsawon lokaci
  • Hashim ya gana da ƴan kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025
  • Ya ce duk da ƙalubalen da PDP ke fuskanta da yadda manyan jiga-jigai ke ficewa daga cikinta, har yanzu jam'iyyar ce kaɗai za ta iya ceto Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ya koma babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP).

Ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da PDP ke fuskanta, har yanzu ita ce kaɗai jam'iyyar da za ta iya ceto Najeriya daga wannan ƙangin.

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim.
Bayan tsawon lokaci, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya koma PDP Hoto: Dr. Gbenga Olawepo-Hashim
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Hashim ya yi wannan furucin ne a wata ganawa da Kwamitin Gudanarwa na PDP (NWC) a hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja, ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya yi murabus daga PDP a zungureriyar wasikar shafi 9

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP za ta iya ceto Najeriya?

Dr. Hashim ya ce duk da kalubale da rabuwar kai da kuma ficewar wasu mambobi a baya, PDP ita ce kadai jam’iyyar ƙasa baki ɗaya da ke da damar ceto Najeriya a 2027.

“Tun da farko, an gina PDP a matsayin wani dandalin siyasa na ƙasa. Tun daga 1998, PDP ke da rinjaye a kusan kowace rumfar zaɓe a faɗin ƙasar nan.
"Wannan tarihi yana nan, wanda hakan ya sa PDP ce kaɗai jam'iyyar da za ta iya kawar da APC daga mulki."
“Kar ku damu da waɗanda suka fice, ƙarfin kowace jam’iyya na tare da yawan jama'arta, ba wai wasu ƴan ƙalilan ba, kuma har yanzu jama’a suna tare da PDP.”

- Dr. Gbenga Olawepo-Hashim.

Hashim ya yabawa shugaban PDP, Damagum

Hashim ya kuma yaba da jagorancin Ambasada Umar Damagun, muƙaddashin shugaban PDP, musamman yadda yake tafiyar da jam’iyyar a cikin mawuyacin lokaci.

Kara karanta wannan

Tsohon mai neman takarar shugaban kasa a APC ya faɗa wa Tinubu gaskiya

“Hikima da kwanciyar hankalin da Damagun ya nuna wajen jagorantar jam’iyyar abin yabo ne. Ya ci gaba da rike jam’iyyar PDP da ƙarfi duk da ƙoƙarin wasu na rusa ta," inji shi.
Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya kai ziyara hedkwatar PDP.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya koma PDP Hoto: @GbengaOH
Source: Twitter

Game da zaɓen shugaban ƙasa na 2027, Dr. Hashim ya buƙaci PDP ta fito da ɗan takara mai nagarta, hangen nesa, wanda zai baiwa batun tsaro, farfaɗo da tattalin arziki da adalci na zamantakewa muhimmanci.

A rahoton Vanguard, Olawepo-Hashim ya ƙara da cewa:

“’Yan Najeriya na fatan samun canjin shugabanci, ina fatan cikin haɗin kai, ladabi da ƙarfin guiwa, PDP za ta tashi tsaye, ba kawai don ta lashe zaɓe ba, sai don ta sake gina Najeriya daga farko.”

Hadimin Atiku ya raba gari da PDP

A wani rahoton, kun ji cewa Demola Olarewaju, ɗaya daga cikin hadiman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga PDP.

A wasiƙar murabus da ya miƙawa shugaban PDP na mazaɓarsa a Legas, ya zargi jam'iyyar da kaucewa aƙidun da aka kafa ta akai tun asali.

Ya bayyana tsarin siyasar APC a matsayin wanda ke janyo rarrabuwar kai, yana mai cewa lokaci ya yi da za a samu hadin kai tsakanin ƴan adawa domin kayar da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262